Pastor ya dauki azumin kwana 40 don koyi ga Annabi Isa, ya mutu ba'a sha ruwa ba
- Wani malamin coci ya mutu bayan yayi azumin kwana 30
- Malamin cocin yabar gida tun a 17 ga wata Yuni
- Mutumin kirki ne wanda yake riko da addinin sa

Asali: Facebook
Wani malamin coci mai suna Alfred Ndlovu a Africa ta Kudu ya rasu a bisa rashin abinci mai gina garkuwa jiki.
Ndlovu yayi alkawarin yin azumi 40 don ya kwaikwayi Allan su, annabi Isa, wanda aka ce haka yayi, sai dai ya rasu bayan yakai azumi na 30.
Wannan malamin coci mai shekaru 44 ya bar gida a ranar 17 ga watan Yuni inda ya fantsama ya shiga daji don gudanar da bauta.
DUBA WANNAN: An sako Kamsilolin Katsina
Ndlovu ya rasu a cikin kwanaki 30 da fara gudanar da ibadar shi inda wasu mutane suka samu gawarshi a cikin jeji inda suka kira jami'an yan sanda.
Malamin cocin mutum ne mai kyautatawa iyalan shi da kuma mutanen yankin sa,yana da ibada wanda mutuwar shi ta bawa kowa mamaki
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng