'Yan Siyasa na barin jama'a da talauci da gangan don su bauta musu - inji wani masani
- Talauci a Najeriya ya kai matsayin Innalillahi
- Rashawa tayi wa 'yan Najeriya katutu
- Cin Hanci shi kanshi rashawa ya zamewa 'yan siyasa halas

Asali: Depositphotos
Farfesa na Tarihin Afrika, Farfesa Toyin Falola ya ce, 'yan siyasa sun saka yan Najeriya cikin yunwa da gan-gan a matsayin dabarar da ze basu ikon juya su a yayin zabe.
Falola, yayin da yake gabatar da lacca da ake kira "Abinci da Mu: Talauci, Siyasa da Harkokin Siyasa" a taron 26 na Kwalejin Aikin Gona na Tarayya, a Abeokuta a ranar Laraba ya kalubalanci jami'o'in Najeriya don karfafa manufofin da ke kare 'yancin kananan manoma da mata da matasa. Ya lura cewa inganta cigaban aikin noma shine tushen nasarar tattalin arzikin kasan.
Da yake magana akan tasirin abinci, Farfesa Falola ya yi kuka da cewa fitar da albarkatun gonaki da shigo da abinci sune barazana ga abincin. "Shigo da abinci, lalacewar muhalli, da kuma talauci ya haifar da yanayin rikice-rikice wanda ke kawo karshen aikin noma da kayayyakin abinci kuma ya haifar da rashin tausayi ga tsarin abinci na kasa".
DUBA WANNAN: Oyedepo dan Illuminati ne - Daddy Freeze\
Ma'aikacin Tarihi, Jami'ar Texas ta Amurka ya kwatanta dogara ga al'ummarsu akan fitar da albarkatun kuɗi da kuma shigo da abinci a matsayin barazanar aiwatar da abinci a Najeriya.
"In akayi la'akari da albarkatun kasa na Nijeriya, be kamata mu zama cikin yunwa ko talauci ba, amma talauci a Najeriya ta kai gagarumin matsayi kuma ana suna fama da yunwa da rashin tsoro".
Ya kara da cewa "Rashin abinci ta ɓata 'yan Nijeriya da dama da suka kasance suna da daraja. Cin hanci da kansa cin abincine da hadiya".
Manyan Dattijai, Farfesoshi da shugabannin Jami'o'i masu fada aji ne suka sami halartar taron.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng