Matar Abiola tayi kaca-kaca da Jonathan, ta fadi dalilin faduwarsa zabe a 2015

Matar Abiola tayi kaca-kaca da Jonathan, ta fadi dalilin faduwarsa zabe a 2015

Zainab Duke-Abiola, matar marigayi Cif Moshood Abiola ta bayyana cewa littafin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rubuta yana cike da karairaki ne da almara kan abubuwan da suka faru a baya.

A ranar Talata 20 ga watan Nuwamban 2018 na Jonathan ya kaddamar da littafinsa mai suna 'My Transition Hours' domin murnar cikarsa shekaru 61 a duniya.

A wata sanarwa da Duke-Abiola ta fitar a ranar Alhamis, ta siffanta littafin a matsayin tsantsagwaron karya. Ta ce abin takaici ne yadda Jonathan ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban Amurka, Barrack Obama da Farai Ministan Ingila, David Cameron sunyi katsalandan cikin zaben 2015.

Matar Abiola tayi kaca-kaca da Jonathan, ta fadi dalilin faduwarsa zabe a 2015
Matar Abiola tayi kaca-kaca da Jonathan, ta fadi dalilin faduwarsa zabe a 2015
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi

"Littafin cike ya ke da karairayi kan batutuwan da suka faru na tarihi.

"Duk da cewa shugaba Jonathan ya amince da shan kaye bayan Buhari ya lashe zabe, har yanzu bai ransa na kan kujerar shugabancin kasar kuma ga kasa amincewa 'yan Najeriya sun tsige shi daga mulki ne saboda ya gaza.

"Gaskiya magana, Jonathan ya fadi zabe ne saboda ya hana kowa fitowa takara duk da gazawarsa. Ya umurce jam'iyyar ta buga kofi daya kacal na fom 001 kuma ya kwace nawa duk da cewa na biya kudi hakan yasa ya rika fada da 'yan siyasa har ta kaishi ga rashin nasarar," inji Duke-Abiola.

Ta ce tsohon shugaban kasar ya jefa Najeriya cikin rikice-rikice da ya janyo rasu rayyuka da tabarbarewar tsaro.

Duke Abiola ta kara da cewa "Abinda ya dace Jonathan ya yi shine ya tuba ga Allah kuma ya nemi gafarar 'yan Najeriya har sai lokacin da suka yafe masa. Babu wani rubuce-rubucen karya da zai sauya irin yadda ya yi wasa da damar da 'yan Najeriya suka bashi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164