Da Obasanjo ya kawo 'Due Process', Atiku ya wahal damu saboda son chuwa-chuwarsa - Obi Eze

Da Obasanjo ya kawo 'Due Process', Atiku ya wahal damu saboda son chuwa-chuwarsa - Obi Eze

- Ana yawan yiwa Atiku kallon dan cuwa-cuwa da kwarapshan

- Atiku ya sha musanta zargin, kuma ba'a taba kaishi kotu ba

- A tsarin duniya sai alkali ya same ka da laifi kake mai laifi, don haka Atiku tsarkakakke ne

Da Obasanjo ya kawo 'Due Process', Atiku ya wahal damu saboda son chuwa-chuwarsa - Obi Eze
Da Obasanjo ya kawo 'Due Process', Atiku ya wahal damu saboda son chuwa-chuwarsa - Obi Eze
Asali: UGC

'Yar takarar kujerar shugaban kasa, kuma tsohuwar Ministar Obasanjo, Obi Ezekwesile, tace daga cikin irin tu'annati da Atiku wai yayi a lokacin Obasanjo lokacin yana mataimakinsa, akwai uwar wahala da ya basu su masu aikin rage cuwa-cuwa a gwamnati.

Da ita da Nasir El-Rufai, Okonjo Iweala, da ma su Ribadu, sune suka kula da tattalin Arzikin Najeriya a wancan lokaci, da gwamnan CBN Soludo.

An dai kawo tsarin Due Process ne kafin a bada kwangila don a cire asarar biliyoyi daga masu kwangila dake cuwa-cuwa, an kuwa yi nasara, sai dai ana samun tsaiko kafin tantance abubuwa, farashi da inda za'a saki kudi.

DUBA WANNAN: Trump na godiya ga Saudiyya don sun rage farashin man fetur

A taronsu na yada manufa a Abuja, Oby Ezeks, mai takara a ACPN, ta dubi wakilin Atiku a wurin taron, inda tace "ko kunsan wannan tahalikin na wakiltar wanda ya wahal damu kan fidda tsarin Due Process" da zai fitar da Najeriya kunya kan barna?"

A cewarta, a lokacin ana kokarin Turawa su yafe wa kasar nan bashi, amma suna so suga mun iya cancana arzikin mu da tattala shi, amma irin su Atiku sunka yi kaka-gida da karfin ikonsu.

Ko a yanzu ma dai, ana zargin Atiku Abubakar, ta hanyar kamfaninsa Intels a bakin gabar Teku, da kin bin tsarin TSA na ajje da biyan dukkan kudaden da gwamnati ke amsa a bankin nai daya na TSA, kuma Hadiza Bala, ta NPA ita ta matsawa kamffanin dole ya bi doka.

Atiku dai nason zama shugaban NAjeriya, kuma yace shi dan Kasuwa ne da bai taba cin haram ba.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng