Duk da kisan gilla, Trump na Amurka na godiya ga masarautar Saudiyya kan farashin man fetur da kudin makamai
- Dan jarida ya rasa ransa amma Amurka tafi son a rage farashi mai
- Zamu cigaba da rage farashin mai inji Shugaban Saudiyya
- Amurka tayi alkawarin zama abokiyar hadin gwiwa da na Saudiyya

Asali: UGC
Shugaban Amurka Donald Trump ya gode wa Saudi Arabia a ranar Laraba don rage farashin man fetur.
"Sun taimakama min wurin maida farashin kasa, yanzu muna da farashi me inganci" Yace.
Wannan jawabin yazo ne ranar da Trump ya bayyana aniyarshi ta ci gaba da tallafawa kasar duk da zargin da akeyi Shugaban Saudi Arabia mai jiran gado, Mohammed Bin Salman na da hannu wurin kisan dan jarida Jamal Kashoggi domin rage farashi man
Kisan na Khashoggi, wani mazaunin Amurka kuma marubuci a jaridar Washington Post ya biyo bayan bacewarsa bayan da aka gayyace shi a Istanbul a ranar 2 ga Oktoba, lamari da ake ganin ya kunyata Washington.
DUBA WANNAN: Hanyoyin moras bankunan Cooperative Society
Shugaba Donald Trump yayi godiya ga Saudi Arabia akan saukaka farashin mai. Washegarin da Amurka tayi alkawarin cigaba da zama abokiyar hadin kai ga masarautar duk da kisan Dan jaridar nan. Wasu dai sunce goyon bayan Trump ga Riyadh saboda saukaka farashin man fetur ne.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump, yayi godiya ga Saudi Arabia game saukake farashin man fetur da kasar tayi. Hakan ya biyo baya ne Washegarin da shugaban kasar Amurka ya tabbatar da hadin kansu ga masarautar Saudi Arabia duk da kashe sanannen Dan jaridar nan da ake zargin ta dashi.
A ranar laraba ne aka samu raguwar farashin man fiye da kashi 6 cikin dari.
Kisan gillar da akayi wa Khashoggi kuma mazaunin US, wanda aka kashe a ofishin jakadancin Saudi Arabia dake Istanbul a ranar 2 ga watan Octoba, ya tozarta Washington.
"Amurka zata cigaba da hada kai da Saudi Arabia don tabbatar da cewa mun bi ra'ayin kasar mu, Isra'ila da sauran yankunan mu" inji Trump.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng