Ba ganawar sirri mu kayi ba: Osinbajo ya yi karin haske kan hotonsa da Obasanjo
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya karyata zargin ganawar sirri da aka ce ya yi da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo saboda wani hoto da ake yadawa a kafafen sada zumunta.
A cikin hoton za a iya ganin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Shugaban Kungiyar yakin neman zaben Buhari, Rotimi Amaechi da kuma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Mafi yawancin mutane suna tsamanin cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara zawarcin tsohon shugaban kasan ne gabanin babban zaben 2019.
Sai dai hadimin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya bayyan gaskiyar lamarin a Twitter inda ya ce an dauki hoton ne a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a yayin da suke gaisawa kafin kowa ya kama gabansa.
DUBA WANNAN: Faifan bidiyo: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a kan tuhumar Ganduje
Ya ce babu wata ganawar sirri da su kayi.
"Kuyi watsi da rahotannin da ke yaduwa na cewa mataimakin shugaban kasa Osinbajo da Minister Amaechi sunyi ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Obasanjo a Ota.
"JIya a filin tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe mataimakin shugaban kasa yana hanyarsa ta zuwa Legas ne suka hadu da tsohon shugaban kasan a yayin shi kuma ya sauka daga jirgi, sun gaisa kuma kowa ya kama gabansa," inji Mr Akande.
DUBA WANNAN: Zan biya N50,000 mafi karancin albashi - Dan takarar shugaban kasa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng