Tsabar soyayya jibi yadda wani maigida yayi wa matarsa da ta maqale a wurin aiki

Tsabar soyayya jibi yadda wani maigida yayi wa matarsa da ta maqale a wurin aiki

- Akwai hanyoyin daban daban na nuna wa juna soyayya

- Ba dole sai ba wa juna kyautuka ba

- Yakamata mutum yasan yanda zai sa mace farin ciki

Tsabar soyayya jibi yadda wani maigida yayi wa matarsa da ta maqale a wurin aiki
Tsabar soyayya jibi yadda wani maigida yayi wa matarsa da ta maqale a wurin aiki
Asali: UGC

Akwai hanyoyin nunawa juna soyayya ga masoya. Ba wai bada kyautuka bane a ranar zagayowar haihuwa, ranar bikin zagayowar haduwar ku da sauransu bane. Yakamata mutum yasa yanda zai farantawa mace rai na daban.

Wani matashi mai suna Dolapo Oni amma anfi kiranshi da Dolarpo ya bayyana yanda ya farantawa matar rai ta hanyar bata mamaki akan hanyarta ta zuwa gida. Mutane kadan ne zasu iya irin abinda yayi.

Kamar yanda yace, matarshi ta makale a cunkoson motoci akan titin Alagomeji dake Yaba, garin Legas, a hanyarta na dawowa gida daga ofishin ta dake Ikoyi. Bayan sunyi magana da mijinta a waya, ta sanar dashi cewa tana Jin yunwa kuma ta gaji.

DUBA WANNAN: Hanyoyin moras bankunan Cooperative Society

Oni, wanda lokacin ya gama shirya dafadukan shinkafa a gida, yayi maza ya diba a kwano, ya hada da abin sha, tare da hawa achaba. Yaje ya nemi motar ta inda ya ganta, ya bata abincin sannan suka suka koma gida tare.

Shin kunsan alaka nawa cunkoson kan titin Legas ya raba? Cunkoson yana kawo kalubale da yawa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng