An rantsar da shugabannin kasa har uku a yau a Bosniya saboda a rage qabilanci

An rantsar da shugabannin kasa har uku a yau a Bosniya saboda a rage qabilanci

- An rantsar da shuwagabannin kasa guda Uku

- Zasu dingayin canji duk bayan wata Takwas

- A watan daya gabata ne aka gudanar da zaben

An rantsar da shugabannin kasa har uku a yau a Bosniya saboda a rage qabilanci
An rantsar da shugabannin kasa har uku a yau a Bosniya saboda a rage qabilanci
Asali: Twitter

A ranar Talata ne Bosnia ta rantsar da shuwagabannin kasar ta su Uku tare da sanya ido akan Milorad Dodik wanda wannan shine karo na farko da zai tafiyar da gwamnati a rarrabe.

Shuwagabannin guda Uku zasu dunga canjin aiki duk bayan wata Takwas dan kawo karshen yakin 1990s Bosnia da kuma bawa kowanne bangare karfi tsakanin Serbs,Croats da kuma musulman Bosnia (Bosniaks).

A watan daya gabata ne masu zabe suka zabi yan kasar don su wakilci yarukan Biyu ganin yanda kabilanci yake neman doke siyasa tun bayan yakin da akayi.

An rantsar da mutane Ukun ne a cikin ginin Sarajevo a gaban tarin jakadodi da yan siyasa.

DUBA WANNAN: Kumallon safe yafi kowanne abinci amfani ga jikin mutum - binciken masana

A 1990s dai an yi ta fadan kabilanci tsakanin Sabiyawa da musulmin Bosnia, inda aka kashe mutane da dama, wanda har saida Amurka, da majalisar dinkin barakar duniya ta kawo wa musulman dauki, aka tarwatsa janar-janar masu son yi musu kisan qare dangi.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng