Yadda Jega ya yi amfani da INEC wajen kayar da ni zabe - Jonathan ya yi fallasa a sabuwar littafinsa
- Goodluck Jonathan ya yi zargin cewa Hukumar Zabe mai Zaman kanta INEC tana da hannu cikin makarkashiyar kayar da shi zabe a 2015
- Jonathan ya ce hukumar ta raba kayayakin zabe a jihohin Arewa zuwa kowanne lungu da sako amma a ta gaza yin hakan a kudancin Najeriya
- Tsohon shugaban kasar kuma ya bayyana dalilai uku da suka sanya ya amince da kayen da ya sha kuma ya kira Buhari ya yi masa murna tun kafin a fadi sakamakon zabe
A sabuwar littafin da ya kaddamar a ranar Talata 20 ga watan Nuwamban 2018, tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta hannu cikin shirya wata makarkashiyar kayar da shi zabe a shekarar 2015.
Premium Times ta ruwaito cewa Goodluck Jonathan ya yi ikirarin cewa INEC ta yi son kai wajen rabon kayayakin zabe tsakanin arewa da kudu kuma hakan shine farkon abinda ya janyo masa shan kaye a zaben da akayi a Mayun 2015.

Asali: Depositphotos
A cikin litafinsa, Jonathan ya rubuta ce: "Saboda wasu dalilai da babu wanda ya sani, INEC ta samu ikon raba katin zabe kusan 100% a arewa, har da arewa maso gabas da ake samun matsalar Boko Haram amma ta gaza yin hakan a kudu duk da cewa akwai zaman lafiya a can."
Tsohon shugaban kasar ya ce ya lura da wadannan matsalolin amma hakan bai sa ya ki aminewa da sakamakon zaben ba.
"Ana ta yada hotuna da bidiyo a kafafen sada zumunta. Sai dai na riga ya yanke shawarar cewa ba zan zama shugaban kasar da zaiyi amfani da wadannan dalilan domin rashin amincewa da sakamakon zabe ba in zargi INEC din da na taimakawa ta tsaya da kafafunta.
"Dukkan duniya ta ga yadda na samu matsala wajen kada kuri'a a mazaba ta saboda na'urar tantance masu zabi tana da matsala.
"Irin wannan matsalar ta faru da mata ta da mahaifiya ta. Wannan abubuwan sun nuna cewa akwai matsaloli tattare da INEC," inji Jonathan.
Ya cigaba da cewa ya amince da kayen da ya sha ne saboda dalilai uku, na farko dai ya bar ma zuciyarsa, na biyu kuma shine baya son hasashen da Amurka tayi na cewa Najeriya za ta ruguje ya zama gaskiya sannan na uku shine kalmar da Buhari ya furta na cewa, za ayi kare jini, biri jini a zaben na 2015.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng