Madalla da aikin Soja: Sojoji sun bindige barayin mutane 14, sun ceto mutane 31 a Kaduna

Madalla da aikin Soja: Sojoji sun bindige barayin mutane 14, sun ceto mutane 31 a Kaduna

Dakarun rundunar sojan kasa sun halaka yan bindiga goma sha hudu dake addabar babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, da hanyar garin Birnin Gwari dake jahar Kaduna, kamar yadda jaridar daily trust ta bayyana.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin shelkwatar Sojojin kasa, Birgediya John Agim ne ya sanar da haka a yayin wata ganawa da yayi da manema labaru a ranar Talata, inda yace Sojoji sun ceto mutane Talatin da daya, 18 kananan yara, 13 manya.

KU KARANTA: Harin ta’addanci: An kashe mutane 50 a yayin bikin maulidi

Agim yace sun samu wannan nasara ne a wani aiki na musamman da suka kaddamar mai taken ‘Operation 777’, inda suka mayar da hankali wajen lalubo mabuyar yan bindiga tare da kwace makamai daga hannunsu.

Bugu da kari kaakakin yace sun kwato dabbobi da dama daga hannuwan yan bindigan, daga ciki akwai shanu 49 da tumaki 42, inda yace tuni sun mika ma masu su bayan an tantancesu duka. Kuma yace akwai sojojin sama da jami’an Yansanda dake taimaka musu a aikin da suka kaddamar.

Wuraren da Sojojin suka fi mayar da hankali sun hada da dajin Kamuku, Kuduru, Birnin Gwari, da Alawa, kuma zuwa yanzu sun kwato manyan bindigu kiar AK-47 guda 18, kananan bindigu 2, da Babura 32, daga hannun yan bindiga, yayin da suka kuma aka raunata musu Sojoji biyu, da yan banga biyu da suka rasa ransu.

“Zuwa yanzu mun kashe yan bindiga 14 da suka hada da masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu, bugu da kari mun kwato muggan makamai da garken shanu daga wajensu, mun ceto akalla mutane 31.

“Mun kama yan binsiga guda biyar, tare da masu basu bayanan sirri guda biyu, wanda a yanzu haka suna bamu karin haske kan yadda suke gudanar da aikin nasu tare da sunayen masu daukan nauyinsu. Amma muma mun yi asarar wasu yan kato da gora guda biyu dake taya mu aiki, da Sojoji biyu da suka jikkata.” Inji shi.

Daga karshe Agim ya tabbatar ma jama’a cewa rundunar Sojiza ta yi iya bakin kokarinta wajen tabbatar da tsaron rayuwar jama’a da dukiyoyinsu domin samar da ingantaccen yanayin zaman lafiya a tsakanin yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng