Jihar da tafi kowacce zaman lafiya a kasar nan - hukumar 'yansanda ta fidda rahoto

Jihar da tafi kowacce zaman lafiya a kasar nan - hukumar 'yansanda ta fidda rahoto

- Yayin da tsaro a arewa ya tabarbare, shi ko na Kudu sai habaka yake

- Enugu tana daya daga cikin Jihohi mafi zaman lafiya a Najeriya

- Ugwuanyi ya cancanci jinjina

Jihar da tafi kowacce zaman lafiya a kasar nan - hukumar 'yansanda ta fidda rahoto
Jihar da tafi kowacce zaman lafiya a kasar nan - hukumar 'yansanda ta fidda rahoto
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar yan sanda (PSC) Alhaji Musiliu Smith a ranar litini ya bayyana cewa Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu ya cancanci jinjina don yanda yake tafiyar da Jihar cikin ci gaba da tsari da kuma tsaro.

Alhaji Smith ya sanar da hakan ne yayin jawabinsa na farko a bikin bude taron kwanaki hudu a Enugu, wanda hukumar ta shirya, don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, yana cewa "da yawanmu muna cikin Enugu saboda Enugu yana daya daga cikin mafi zaman lafiya a cikin kasar ".

Tsohon Janar na 'yan sanda ya ce gwamnan ya cika alkawarin da ya dauka wajen karfafa dangantakar gwamnati da yan sanda a jihar, wanda ya kasance me amfani ga mutanen Enugu da 'yan sanda

A cikin jawabin nasa, tsohon Janar din yace, "Gwamnatin Jihar Enugu, jagorancin Babban Gwamna, Rt. Hon. Ifeanyi Ugwuanyi, dole ne a yaba mishi abin farin ciki ne don na lura cewa ya tallafa wa hukumar yan sanda. Don haka, a madadina da ma'aikatan hukumar, na yaba da nuna godiya ga Mai girma, Gwamna da mutanen Jihar Enugu".

DUBA WANNAN: Amnesty da HURIWA na takurawa yaki da ta'addanci

Yayin da yake jawabin bude taron, Gov. Ugwuanyi, wanda ya yi marhabin da Shugaban, da sauran mambobi da ma'aikatan hukumar Enugu, ya jaddada cewa "kare lafiyar rayuka da dukiyar jama'armu da kuma kiyaye zaman lafiya a duk fadin jihar shine tsari da manufar gwamnatinmu ".

Gwamna Ugwuanyi, wanda wakiliyarsa, Misis Cecilia Ezeilo ta wakilta, ya bayyana cewa, gwamnatinsa tana da kyakkyawan haɗin gwiwa da 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a jihar. Ya kara da cewa, "Muna farin ciki da yadda Jihar Enugu ta kasance daya daga cikin mafi aminci, kwanciyar hankali da mafi yawan zaman lafiya a Najeriya a yau".

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng