Kungiyoyin 'yancin dan-adam na takura ma harkar yaqi da ta'addanci - Sojin Najeriya

Kungiyoyin 'yancin dan-adam na takura ma harkar yaqi da ta'addanci - Sojin Najeriya

- An cafke yan ta'adda 14 a karon da sukayi da rundunar sojoji

- An kubutar da shanye 422 da tumakai tun daga watan Octoba zuwa yanzu

- Muna da wakilci daga ko'ina sassa na kasar nan

Kungiyoyin 'yancin dan-adam na takura ma harkar yaqi da ta'addanci - Sojin Najeriya
Kungiyoyin 'yancin dan-adam na takura ma harkar yaqi da ta'addanci - Sojin Najeriya
Asali: Depositphotos

A lokuta da dama, ana saun matsalolin kare ko cin mutumci da hakkin bil-Adam a yakoki da ake yi a duniya, kuma akwai kungiyoyi masu sanya idanu kan yadda lamarin ke tafiya.

Amnesty International, da Human Rights Watch, sunyi suna wajen neman soji su girmama dokar kasa wajen yakinsu da mayakan ta'adda.

Yawanci 'yan ta'addan basu girmama dokokin duniya, kuma suna fakewa da dokar da soji ke bi wajen aikata barnarsu.

Yanzu dai sojin Najeriya sun koka, inda suka ce kungiyoyin na hana su fatattakar 'yan ta'adda saboda suna cewa ma cin zalinsu ake yi.

Mukaddashin daraktan labarai na tsaro, Birgadiya Janar John Agim, ya kuma ce yada karya game da sojin Najeriya don dakushe darajar rundunar ne dake yaki da ta'addanci.

DUBA WANNAN: Atiku zai dara idan suka hada kai Yarabawa da Igbo

Agim, wanda ya tattauna da manema labarai akan yanda suka cafke yan ta'adda 14 a wani karon da sukayi da rundunar. Shanaye 422 da kuma tumakai aka samu daga samamen da suka fara tun a watan Octoba 2018.

"Sojin Najeriya da sauran jami'an tsaron Najeriya an samo su ne daga kowanne bangare na Najeriya. Wannan na nuna cewa muna da wakilai a ko ina." inji mai magana da yawun daraktan tsaro.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng