Kumallon safe yafi kowanne abinci amfani ga jikin mutum - binciken masana
- Karin kumallon safe yanada matukar muhimmanci
- Yana taimakawa wajen maida hankali a bangaren karatu
- Idan jikin dan adam bai samu abinci ba hakan na janyo mishi karancin kuzari

Asali: Getty Images
Karin kumallon safe yana da matukar muhimmaci a jikin dan adam,yana taimakawa jiki wajen saisaita abincin da zakaci a rana,sannan yana taimakawa wajen bada kuzari dan aiwatar da abubuwan daya kamata.
Dadin dadawa Karin kumallon safe yana taimakawa mutum ya maida hankali akan aikin shi ko kuma karatu,wannan dalili yasa ake ganin shine yafi duk wani abinci muhimmanci.

Asali: Depositphotos
Mafi yawan bincike ya nuna cewa karin kumallo yana kara lafiya,wanda ya hada da karancin damar kamuwa da ciwon suga,cutukan zuciya da kuma shahararriyar kiba.
Akwai sirrika masu tarin yawa a cikin yin karin kumallon zai taimaka wajen ka gudanar da ranar ka cikin jindadi da walwala.
DUBA WANNAN: Amnesty da HURIWA na takurawa yaki da ta'addanci
Farawa da karin kumallo kan iya samar da natsuwa ga jikin Dan Adam Na Tsawon yini. Yana samar da karfin jiki wanda hakan ke taimako na yin kujiba-kujiba a wurin aiki ko kuwa makaranta. Wadannan kadan kenan daga cikin amfanin karin kumallo a jikin Dan adam. Bincike ya nuna cewa yin karin kumallo yana samar da lafiyar jiki da kuma zurfin tunani.
Mutane da yawa kan tsallake karin kumallo, wanda hakan kuskure ne. Dan adam na bukatar abinci tun safiya.
Karin kumallo kan taka rawar gani gurin saisaita kibar mutum. Masu bincike sun gano cewa mutanen da ke karin kumallo suna da sirarantaka fiye da marasa ci.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng