Kurungus! Atiku ya bayyana wanda zai sayar ma kamfanin NNPC idan ya zama shugaban kasa

Kurungus! Atiku ya bayyana wanda zai sayar ma kamfanin NNPC idan ya zama shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya tabbatar da burinsa na sayar da kamfanin man fetir na Najeriya da matatun man fetir guda hudu na Najeriya gaba daya don samun isassun kudade a Najeriya.

Kaakakin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Segun Sowunmi bayyana haka a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, inda yace idan har Atiku Abubakar ya samu nasara a zaben 2019, zai sayar da matatun man fetir gaba daya, yan Najeriya zai sayar ma wa.

KU KARANTA: Tashin hankali: Yadda wani ‘Da’u fataken dare’ ya yi awon gaba da Mota daga ofishin Yansanda

Kurungus! Atiku ya bayyana wanda zai sayar ma kamfanin NNPC idan ya zama shugaban kasa
Atiku
Asali: Twitter

Sowunmi yace idan aka yi duba ga kamfanin man fetir na Oando, ko kamfanin wayar tarho ta Glo za’a ga cewa yan Najeriya suna da kwarewa kuma sun yi kwarin da zasu iya tafiyar da babban kamfani irin NNPC, don haka yan Najeriya zasu sayar ma kamfanin man fetir na Najeriya.

A cewar Sowunmi gwamnati bata da hurumin gudanar da kasuwanci, amma gwamnati ya kamata ace ta samar da tsare tsare, dokoki da sa ido da zasu kara kaimi ga harkokin kasuwanci tare da tabbatar da samun riba mai yawa.

Atiku Abubakar ya bayyana wadanda zai sayar ma kamfanin matatar man fetir ne biyo bayan tambayar da wani hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bismarck Rewane yayi masa, inda yace ya kamata yan Najeriya su san suwanene zai sayar ma NNPC.

A jawabinsa, Rewane yace ya gamsu da ra’ayin Atiku na sayar da NNPC, amma damuwarsa shine wa zai sayar mawa idan har ya zama shugaban kasa, don kuwa idan bai bi a hankali ba zai fada cikin rikici da badakala.

“Abinda ya kamata shine a maimakon gwamnati ta mallaki NNPC, kamata yayi ace ya zama kamfanin Najeriya amma yan kasuwa ne ke rike dashi, suke tafiyar dashi, sai a bar wani kaso ga gwamnatin tarayya ta rike.

“Ya kamata mu san su wa da wa zai sayar ma NNPC, kuma ta yaya zai tabbatar da cewar bai sayar ma abokansa ba, saboda mu kauce ma irin matsalar kasar Rasha, wanda ta sayar da kamfanin manta amma ga yan kasuwa wadanda suke cikin gwamnati, don haka suke kare bukatunsu a madadin bukatun kasar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel