Abdulsami, 'Kusoshin Gwamnati da suka halarci Bikin kaddamar da Littafin tsohon shugaban kasa Jonathan
Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soji, Abdulsalami Abubakar da kuma takwaransa Yakubu Gowon, na cikin manyan jiga-jigan kasar nan da suka halarci bikin kaddamar da littafin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan.
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, kusoshi da manyan baki na kasar nan sun yi dandazo a harabar babban Hotel din nan na Transcorp Hilton da ke garin Abuja domin karrama bikin kaddamar da littafin tsohon shugaban kasar na Najeriya.
Tsohon shugaban kasar tare da mai dakinsa, Patience Jonathan, sun isa harabar wannan babban taro da misalin karfe 11.45 na safiyar yau inda farfajiyar ta dunke da yi ma su lale marhabun.
A yayin da tsaro ya tsananta a wannan haraba, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya samu kyakkyawar tarba da ta dauki hankali yayin isowar sa, inda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari da bai samu halarta ba.

Asali: Depositphotos
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo tare da tsaffin Ministoci da kuma sarakunan gargajiya, tuni sun hallara a wannan haraba yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da kai ruwa rana ta kiciniyar shawo kan al'umma da ke kokarin kashe kwarkwatar idanunsu.
Da misalin karfe 12.00 na ranar yau ta Talata aka fara gudanar da bikin kaddamar da wannan fittacen littafi na Jonathan mai taken "Sa'o'in da na mika mulki" da a turance yake "My Transition Hours", inda ya samu halarcin shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da kuma Mataimakin sa, Ike Ekweremadu.
KARANTA KUMA: Ni zan yi nasara kan Buhari da Atiku a zaben 2019 - Olawepo Hashim
A yayin wannan gagarumin taro da ya kasance wani bigire na shagulgulan bikin murnar cikar Jonathan shekaru 61 a duniya, gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson, ya bayar da tallafin N100m da kuma katafaren fili ga gidauniyar nan ta Goodluck Ebele Jonathan Foundation.
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon shugaban kasa Abdulsalami yayin gabatar da jawabansa ya yabawa Jonathan dangane da tawali'unsa da kuma daukar dangana yayin da ya sha kashi a zaben shugaban kasa na 2015, inda hakan ya tabbatar da soyayyarsa da kuma kishin kasar nan da ta mamaye zuciyar sa.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng