Hadakan Sojojin Najeriya da jaruman matasan Borno sun raka yan Boko Haram har gida

Hadakan Sojojin Najeriya da jaruman matasan Borno sun raka yan Boko Haram har gida

Dakarun rundunar Sojan Najeriya tare da hadin gwiwar kungiyar jaruman matasan jahar Borno wanda aka fi sani da suna Civilian JTF sun yi ma mayakan Boko Haram rakiyan kura bayan wani hari da suka kai a kauyen Mammanti na jahar Borno.

Legit.com ta ruwaito hadakan Sojojin sun afka cikin dazukan da mayakan na Boko Haram ke samun mafaka tare da taimakon mafarautan yankin, a kokarinsu na kakkabe ragowar yan ta’addan Boko Haram dake kai hare hare a yankin.

KU KARANTA; Gwamnan Kano ya lashe kyautar gwarzon gwamnan nahiyar Afirka kwata

Hadakan Sojojin Najeriya da jaruman matasan Borno sun raka yan Boko Haram har gida
Sojoji
Asali: UGC

Shelkwatar rundunar Sojan kasa ta sanar da cewa Sojojin sun ratsa kauyuka da dama a wannan samame da suka kai, da suka hada da Kamari, Koyamti, Durwala, Ajiri, da Tumballa, inda suka tabbatar sun kakkabe duk wani dan Boko Haram dake fakewa a kauyukan.

A yayin da suke wannan aiki na kakkabe mayakan yan ta’adda, Sojojin sun tabbatar ma jama’a mazauna kauyukan da tsaronsu, inda suka bukaci da suka cigaba da harkokinsu na yau da kullum saboda suna cikin aminci tsundum.

A wani labarin kuma, babban hafsan rundunar Sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya tura da sabbin dakarun Sojojin Najeriya na musamman zuwa filin daga dake yankin Arewa maso gabas, kamar yadda jaridar Legit.com ta ruwaito.

Hadakan Sojojin Najeriya da jaruman matasan Borno sun raka yan Boko Haram har gida
Hadakan Sojojin Najeriya da jaruman matasan
Asali: UGC

Shelkwatar sojan kasa ta bayyana manufar tura wadannan dakaru na musamman Arewa maso gabas shine don su fafata da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, musamman a jahar Borno domin a samu nasarar kawo karshen yaki da ta’addanci da aka dade ana fafatawa.

Dakarun Sojin sun tafi ne dauke da kayansu, da kuma manyan makamai da zasu taimaka musu wajen yakar mayakan yan ta’addan, wadanda a yanzu haka suke cigaba da kai farmaki a garuruwa daban daban na jahar Borno.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng