PDP 2019: Jiharmu tafi albarka tun da muka bar APC muka koma PDP

PDP 2019: Jiharmu tafi albarka tun da muka bar APC muka koma PDP

- Tun lokacin da nabar APC na samu yanci

- A lokacin da nake cikin jam'iyar bana iya biyan ma'aikata hakkin su

- Babu wani sauran mulkin kama karya a jihar

PDP 2019: Jiharmu tafi albarka tun da muka bar APC muka koma PDP
PDP 2019: Jiharmu tafi albarka tun da muka bar APC muka koma PDP
Asali: Depositphotos

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortum yace tun lokacin da yabar jam'iyar APC ya samu yancin Kansa. Gwamnan yace mulkin kama karya da akeyi a jam'iyar bai barshi ya samu yanci ba. Yayi wannan bayani ne a lokacin da yake nada kwamishinoni guda 9 a Makurdi.

A halin yanzu ina samun damar biyan ma'aikata albashin su akan kari sabanin lokacin da nake jam'iyar APC bana samun wannan damar. Gwamnan ya kara da cewa babu wani sauran mulkin kama karya a jihar tasa ta Benue saboda sun samu yanci tun bayan komawar sa PDP.

"Tunda na bar APC nake biyan ma'aikata albashin su," inji Ortom. A cewar shi, siyasar ubangida ta jam'iyyar APC ta hana shi taka rawar gaban hantsi. "Babu ubangida a jihar Benue" inji Ortom

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, yace tunda ya bar jam'iyyar APC yake biyan ma'aikata albashin su. Kamar yanda gwamnan yace, siyasar ubangida ta jam'iyyar APC ta hana shi taka rawar gaban hantsi.

Ya fadi hakan ne yayin rantsar da kwamishinoni tara a Makurdi, babban birnin jihar. Ortom yace, babu siyasar 'ubangida a jihar Benue' a karkashin mulkin shi. Yace tunda ya koma jam'iyyar PDP ya samu sakat har yake biyan albashi.

DUBA WANNAN: Bincike yace wadanni suna da saurin fushi

"Babu siyasar ubangida yanzu a jihar Benue karkashin mulki na. Zaku ga tunda na raba kaina daga ubangidana, har albashi nake biya akan lokaci, " inji shi.

"Ina neman wasu hanyoyin biyan basussukan albashi da ake bina. Lokacin da nake APC, iyayen gidana bazasu barni inyi abinda nake so ba."

A yanzu dai, gwamnoni a yawa da ma 'yan majalisu, sun sauya sheqa, inda suka koma jam'iyyun adawa domin kuntata wa gwamnatin APC, da ma kuma cewa zabe ya taho, kowa na neman farantawa jiharsa ko talakawansa rai.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng