2019: 'Babu wasu 'yan takara a jihar Borno'

2019: 'Babu wasu 'yan takara a jihar Borno'

- Jam'iyyar PDP bata da Dan takarar gwamna a jihar Borno

- Sai dai idan INEC zata dubi karamin ministan wuta, Mohammed Wakil

- Duk da dai an fitar da sunan Alhaji Mohammed Imam a matsayin Dan takarar gwamnan jihar

2019: 'Babu wasu 'yan takara a jihar Borno'
2019: 'Babu wasu 'yan takara a jihar Borno'
Asali: Facebook

Wata kungiyar tallafin jam'iyyar PDP, Yerwa Oodua, tace jam'iyyar bata da tsayayyen Dan takarar kujerar gwamnan jihar Borno da kujerar sanata mai wakiltar jihar ta tsakiya.

A taron manema labarai da sukayi a ranar litinin, a Ikeja, jihar Legas, shugaban kungiyar, Bakura Goni-Makinta da sakataren shi Mustapha Mustapha, sunce sai dai Idan hukumar zabe mai zaman kanta zata dubi tsohon karamin ministan wuta, Mohammed Wakil, a matsayin Dan takarar gwamnan da kuma tsohon kakakin majalisar jihar, Bukar Kachallah, a matsayin Dan takarar kujerar sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya. Wanda Idan hakan bata faru ba, jam'iyyar zata iya rasa kujerun.

DUBA WANNAN: An fara kauracewa majalisa

"Duk da dai, INEC ta fitar da sunayen Alhaji Mohammed Imam a matsayin Dan takarar gwamnan jihar da kuma Sanata Abba Aji a matsayin Dan takarar kujerar sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya. Amma ba tsayayyun yan takara bane, domin zaben fidda gwanin da akayi nasu ba bisa ka'ida bane kuma wata kwamiti ce karkashin jagorancin Alhaji Zannah Gaddama, ta shirya.

A watanni biyu da suka wuce, wata kotun tarayya dake jihar Maiduguri ta yanke hukuncin cewa kwamitin zababbun jam'iyyar PDP ta jihar Borno na karkashin jagorancin Alhaji Usman Bade ne."

"A karkashin jagorancin Alhaji Usman Bade ne akayi zaben fidda gwanin da ya samar da Mohammed Wakil da Alhaji Bukar Kachallah. Muna da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba kotu zata tabbatar da hukuncin ta ta hanyar ba wa INEC umarnin fitar da sunayen Mohammed Wakil da Bukar Kachallah a matsayin yan takarar jam'iyyar." inji Goni-Makinta

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng