Da qyar muka juyo akalar kasar nan daga barna da sakacin Jonathan - Osinbajo
- An kwaci mulki da quri'u daga hannun PDP a 2015
- An taras da dumbin bashi a lalitar gwamnati
- An zargi GEJ da ciwo basukan banza

Asali: Depositphotos
Duka da irin dumbin aiki da gwamnatin Jonathan tayi a NAjeriya daga 2010 zuwa 2015, ya zuwa yanzu Osinbajo na APC yace babu wani katabus da suka yi banda ciwo wa kasar nan bashi, sakaci, da almundahana da kudaden gwamnati.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya kushe tsohuwar gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan, cewa da ta ginu ne bisa ga tsantsar rashawa.
Osinbajo yace ya firgita da yawan rashawa da ta mamaye tsohuwar gwamnatin.
Mataimakin shugaban kasan yace abin mamaki ne ace a rana daya an kwashe dala miliyan 292, kimanin Naira biliyan 70 daga babban bankin Najeriya ba tare da wani bayanin kwangila ba.
Kamar yanda yace abin mamaki ace bayan samun dala biliyan 381 daga man fetur tsakanin 2010 zuwa 2014, asusun waje ya fadi zuwa dala biliyan 30 a 2014 kuma gwamnatin Jonathan ta bar bashin dala biliyan 63.806.
Ya kara da cewa, tsakanin 2010 zuwa 2015, bashin da ake bin Najeriya ya tashi daga dala biliyan 35,093.10 zuwa dala biliyan 63, 806.53.
Daga 2010 zuwa 2014, bashi ya tashi daga dala biliyan 35 zuwa dala biliyan 63. Koda muka hau kan kujerar mu, bashin da muka tarar ya kai dala biliyan 63. Inji Osinbajo.
"A yau, shekaru 3 da rabi, bashin kasar na ya kai dala biliyan 73. Akwai dalilai biyu da suka sa har yau muke cikin talauci, na daya shine tsananin rashawa da kuma sakaci. Akwai bambanci tsakanin rashawa da tsananin rashawa, wacce ita ce ke addabar kasar Najeriya.
DUBA WANNAN: Babu dan takara a jihar Borno a PDP
Ba'a dai taba samun kudi masu yawan na wannan tsakanin ba, musamman ganin kasuwar mai tayi ba'in tashi, saboda yake-yake da kasashen larabawa ke tayi, da ma barazanar yaki da Iran da Amurka.
Ana dai ta cacar baki tsakanin APC da PDP, kan wa yafi kawo wa juna matsala a ko sharri a lokacin yakin neman zaben shuwagabanni a 2019.
Shi dai Osinbajo, yana ta rabon kudi ga talakawa, jarin 10,000 ga duk wanda ke bukata, domin agazawa kananan 'yan kasuwa.
An zargi dai shugaba Buhari da ciwo bashn da tuni ya zarta na Jonathan, ida gwamnatin tace ai aiki take manya-manya da kudin.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng