Takai ya samu rashin goyon baya daga wani bangaren PRP a Jihar Kano

Takai ya samu rashin goyon baya daga wani bangaren PRP a Jihar Kano

Mun samu labari cewa wani bangare na Jam’iyyar PRP a Jihar Kano sun nuna rashin amincewar su game da tsaida Salihu Sagir Takai da aka yi a matsayin ‘Dan takarar Gwamna na Jam’iyyar a 2019.

Takai ya samu rashin goyon baya daga wani bangaren PRP a Jihar Kano
‘Yan Taware a Jam’iyyar PRP ba su yi amanna da takarar Takai ba
Asali: UGC

Shugaban wannan bangare na ‘Yan Taware a Jam’iyyar watau Alhaji Mukhtar Zango ya bayyanawa manema labarai a Ranar Lahadin nan cewa ba su yi na’am da matakin da Jam’iyyar ta dauka farat daya na ba Malam Salihu Takai tikiti ba.

Mukhtar Zango ya koka da cewa ana kokarin fisge Jam’iyyar daga hannun su bayan sun yi shekaru kusan 27 su na hidima da ita a Kano. Zango ya kuma bayyana cewa yana cikin na-kusa da Malam Aminu Kano wanda ya kafa PRP.

KU KARANTA: 2019: Jam’iyyar PRP ta canza ‘Dan takarar Gwamna a Jihar Kano

Shugaban wannan bangare na Jam’iyyar, ya zargi wata Kungiya mai zaman kan-ta da amfani da kudi wajen ba Salihu Takai tutan takarar Gwamna na Jihar Kano a zaben da za ayi shekarar badi bayan ya sha kasa a Jam’iyyar adawa ta PDP.

Har wa yau, Alhaji Zango ya bayyana cewa an tsige shugabannin Jam’iyyar na Kananan Hukumomi 44 wanda hakan ya sabawa umarnin da Jigon Jam’iyyar watau Balarabe Musa ya bada. Zango yace don haka ba su san da zaman Takai ba.

Shugaban Jam’iyyar ta PRP a Kano Shariff Sammani ya bayyanawa Jaridar Daily Nigerian cewa bai san da wannan bangare na Mukhtar Zango ba, inda ya kara da cewa an bi tsari wajen ba Malam Takai tuta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng