Kwankwaso ya ziyarci Iyalan Marigayi ‘Dan Masanin Kano da Isiyaka Rabiu
Mun samu labari cewa a jiya Litinin 12 ga Watan Nuwamban nan ne Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci Iyalan Marigayi Air Vice Marshal Mukhtari Muhammad wanda ya rasu kwanakin baya a cikin Garin Kano.

Asali: UGC
Tsohon Gwamnan ya samu ganawa da Mai dakin Marigayin inda ya mika ta’aziyyar na wannan babban rashi da aka yi a baya. Kafin nan kuma dai Injiniya Rabiu Kwankwaso ya kai irin wannan ziyara gidan Marigayi Dan Masanin Kano.
Sanatan wanda yanzu haka yana Jihar Kano yayi amfani da wannan dama ya gana da Iyalan da Marigayi Yusuf Maitama Sule ya bari. Tsohon Gwamnan yayi wannan ziyara ne tare da ‘Yan takaran PDP a zabe mai zuwa na 2019.
KU KARANTA: Buhari yayi magana kan bidiyoyin zargin cin hancin Ganduje
A ko ina dai tsohon Gwamnan ya sa kafa, yana tare da Abba Kabir Yusuf da kuma Aminu Abdussalam Gwarzo wanda za su rikewa PDP tuta a 2019. Kwankwaso ya kuma ziyarci gidan Dattijon nan na Kano watau Bashir Tofa a gidan sa.
Sanata Kwankwaso ya leka har fadar Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II amma ya bayyana cewa ganawar da ta fi burge sa shi ne haduwar da yayi da wasu Matasa da ya tura Kasar waje domin su yi karatun Digiri na PhD.
Wadannan ‘Dalibai sun hada Dr. Aliyu Isa wanda ya karanci lissafi a Kasar Turkiya da kuma Dr. Muhammad Bashir wanda ya samu Digiri na uku a kan fannin fasahar wuta da kuma ‘Dan uwan sa Dr Gaddafi Sani wanda yayi karatu a Sin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng