2019: PDP ta yiwa APC tumbur a mazabar Atiku

2019: PDP ta yiwa APC tumbur a mazabar Atiku

Rabaran Habila Istifanus, wani fitaccen dan siyasa daga kudancin jihar Adamawa, ya jagoranci mambobin jam'iyyar APC fiye da 30,000 wajen canja sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fito ne daga sanatoriyar kudancin jihar Adamawa.

Da ya ke magana da manema labarai yau, Litinin, a Yola, Istifanus ya yi alla-wadai da zaben fidda 'yan takara na APC tare da bayyana shi a matsayin wasan yara.

Istifanus ya nemi am'iyyar APC ta tsayar da shi takarar kujerar majalisar wakilai mai wakiltar Toungo/Ganye/Jada/Mayobelwa amma sai dan majalisar yankin, Abdulrazak Namdas, ya kayar da shi a zaben cikin gida.

2019: PDP ta yiwa APC tumbur a mazabar Atiku
Atiku
Asali: UGC

"Na kashe fiye da miliyan N22m domin sayen fam din takarar majalisar wakilai a jam'iyyar APC, amma sai shugabancin jam'iyyar ya wofantar da mu tare da bawa dan takarar da su ke so tikitin takarar kyauta," a cewar Istifanus.

Sannan ya cigaba da cewa, "yanzu mun yanke shawarar fita daga jam'iyyar rashin adalci, ni da magoya baya na fiye da 30,000 za mu yiwa 'yan takarar PDP a matakin jiha da na tarayya aiki a zaben shekarar 2019."

DUBA WANNAN: Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna

Dan takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar PDP, Umar Fintiri, ne ya karbi ma su canja shekar tare da bukatar su hada kai da mambobin PDP domin kawo karshen gwamnatin APC.

"Ni ne halastaccen dan takarar gwamna," Fintiri ya fada cikin yanayin habaici ga gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindo, da ke fama da badakalar takardun karatu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng