Da dumi dumi: Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da sabon kwamandan rundunar yaki da Boko Haram

Da dumi dumi: Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da sabon kwamandan rundunar yaki da Boko Haram

Rundunar Sojan kasa ta sanar da nadin sabon kwamandan dakarun Sojojin Najeriya dake yaki da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram sakamakon yawaitan karuwar hare haren yan ta’adda a yankin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito shugaban hafsoshin rundunar Sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ne ya nada sabon kwamandan mai suna Manjo janar Benson Akinroluyo, kamar yadda sanarwar daga shelkwatar rundunar Soja ta sanar.

KU KARANTA: Babban bankin Najeriya ta bayyana wadanda suka fi taurin bashi tsakanin Maza da Mata

Manjo janar Abba Dikko ne ya mika ragamar iko ga Akinroluyo a ranar Lahadi 11 ga watan Nuwamba, wanda haka ya sanyashi zama kwamanda na biyar da ya taba jagorantar Sojojin Najeriya a yaki da yan ta’adda.

A watan Yuli daya gabata ne aka nada Dikko mukamin kwamandan yaki da Boko Haram, amma tun bayan darewarsa mukamin aka dinga samun hare haren yan ta’adda a barikokin Sojoji da sansanoninsu.

Sai dai ana danganta hare haren ga bangaren kungiyar Boko Haram da suka yi mabaya’a ga kungiyar ta’addanci ta Duniya, ISIS, watau kungiyar kafa daular musulunci a yankin yammacin Afirka (ISWAP).

Alkalumma sn tabbatar da cewa daga shekarar 2009 zuwa yanzu an samu rashe rashen rayuka sama da dubu ashirin da bakwai (27,000) tare da mutane miliyan biyu da suka tsere daga gidajensu a dalilin yakin.

Kuma har yanzu ana samu hare haren Boko Haram duk da cewa gwamnatin Najeriya na ikirarin wai ta karya kungiyar Boko Haram, don kuwa ko a ranar Asabar din data gabata kungiyar ta kai hari a kauyen Jimmi dake jahar Borno, inda suka kashe mutane, tare da kona gidaje da satar dabbobi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng