Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70, hotuna

Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70, hotuna

A yammacin yau, Lahadi, ne shugaba Buhari ya gabatar da jawabi ga taron shugabannin kasashe kusan 70 a kasar Faransa.

Buhari ya gabatar da jawabin a dakin taro na 'Grande Halle de la Vilette' inda ya yi magana a kan 'cin hanci da kwararar kudin almundahana'.

Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70, hotuna
Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70
Asali: Facebook

Kafin gabatar da jawabin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci wani taron cin abinci da aka shirya domin karrama shugabannin kasashen duniya da ke halartar wani taro na kasa da kasa a kan inganta zaman lafiya a kasar Faransa.

Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70
Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya samu damar ganawa da babban sakataren majalisar dinkin duniya (MDD), Antonio Guterres, da ragowar shugabannin kasashe da dama domin tattauna yadda za a hada karfi da karfe domin samun zaman lafiya a kowanne bangare na duniya.

DUBA WANNAN: Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna

A daren jiya, Asabar, ne jaridar Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Faransa domin halartar taron kasa da kasa a kan zaman lafiya da za a yi, a karo na farko, tsakanin ranakun 11 da 13 ga watan Disamba, 2018.

Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70, hotuna
Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70
Asali: Facebook

A sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasa a jiya, Juma'a, Femi Adesina, kakakin shugaba Buhari ya sanar da cewar Buhari zai sadu da babban sakataren Majalisar dinkin duniya da ragowar shugabannin duniya domin tattauna gudunmawar da kowa zai iya bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70, hotuna
Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya 70
Asali: Facebook

Buhari zai halarci taron cin abinci da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya shiryawa ragowar bakin da su ka halarci taron. Buhari, bayan ya sauka a kasar Faransa Gwamnatin kasar Faransa da hadin gwuiwar wasu kungiyoyi ne su ka shirya taron domin tattaunawa a kan muhimman batutuwan da zasu tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Daga cikin 'yan rakiyar shugaba Buhari akwai; gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, gwamna Willie Obiano na jihar Anambra, da gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti.

Ragowar 'yan rakiyar su ne; ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; ministan shari'a, Abubakar Malami; mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Babagana Monguno; da babban darektan hukumar leken asiri ta kasa, Ahmed Abubakar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng