Shugaban Hafsun Soja yayi wasu canje-canje a Rundunar Sojojin Kasa
Mun samu labari daga bakin Darektan yada labarai na Sojojin kasan Najeriya Birgediya Janar Texas Chukwu cewa an yi wasu sauye-sauye a gidan Sojan wanda ya shafi manyan Jami’ai fiye da 100.

Asali: Twitter
Yanzu haka an nada Mataimakin Shugaban sabuwar Jami’ar Sojoji da aka gina a Garin Biu da ke Jihar Borno. Daga cikin wadanda Shugaban Hafsun Sojin kasar Janar Tukur Buratai ya canza akwai Shugaban Rundunar Operation Lafiya Dole.
Rundunar Sojin ta cire Manjo Janar Abba Dikko daga Operation Lafiya Dole zuwa wani bangaren. Birgediya Janar Ifiok Obot wanda yake kula da Rundunar Operation Delta Safe ne aka nada a matsayin Mataimakin Shugaban sabuwar Jami’ar Biu.
Daga cikin wadanda aka sauyawa wurin aiki kuma akwai Manjo Janar Victor Ezugwu wanda aka dauke daga Zaria. Shi ma dai Manjo Janar Adeyemi Adetayo, an canza masa wuri daga ASCON inda aka nada sa Darektan shigo da kaya a babbar Hedikwata.
KU KARANTA: Hotunan irin tarbar da aka yi wa Shugaba Buhari a kasar waje jiya
Sauran Birgediyoyin Janar irin su Olufemi Dada sun koma bangaren TRADOC yayin da Solomon Udounwa ya koma Hedikwata a Abuja. Haka kuma Adekunle Adesope, Nasiru Jega, Sani Mohammed da kuma Kabir Mukhtar sun zama manyan Darektoci.
Manjo Janar Jamil Sarham zai cigaba da zama Hedikwata ta 6 yayin da Manjo Janar Nuhu Angbazo ya zama sabon GOC na Hedikwata ta 3. Shi kuma Manjo Janar Benson Akinroluyo ya canji Dikko a matsayin Jagoran Operation Lafiya Dole a Borno.
Wadanda wannan sauye-sauye ya shafa sun hada manyan Janorori masu taurora guda irin su Kevin Aligbe. An kuma taba auran Jami’ai irin su Kanal Kingsley Umoh, Adamu Nura, Louis Lepdung da Kanal Kayode Ogunsanya a wannan canjin da aka yi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng