Idan mu ka kira Ambode a waya don mu taimake sa a APC ba ya dauka - Adefuye

Idan mu ka kira Ambode a waya don mu taimake sa a APC ba ya dauka - Adefuye

Labari ya iso mana cewa Anthony Adefuye wanda yana cikin manyan Jam’iyyar APC a Jihar Legas ya bayyana irin kokarin da su kayi na sasanta Gwamna Akinwumi Ambode da kuma Asiwaju Bola Tinubu.

Idan mu ka kira Ambode a waya don mu taimake saa APC ba ya dauka - Adefuye
Adefuye yace Gwamna Ambode ya jefa kan sa cikin matsala
Asali: Depositphotos

Anthony Adefuye wanda daya ne daga cikin Majalisar GAC masu ba Gwamna shawara a Legas yace yayi bakin kokari wajen dinke barakar da ta shigo Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar wanda tayi sanadiyyar Gwamna Ambode ya rasa tikiti.

Adefuye yace sun nemi su ga Gwamna Akinwumi Ambode ya samu tikitin tazarce a APC, akasin abin da mutane ke rayawa na cewa sun hana sa zarcewa. Jigon Jam’iyyar yace sun nemi su gana da Gwamnan a lokacin amma abin ya faskara.

Babban ‘Dan siyasar yace duk kokarin da su kayi na saduwa da Gwamna Ambode a lokacin ana tsakiyar rikicin zabe ya ci tura. Adefuye yace sun dade da hango cewa Ambode zai samu matsala a zaben APC don haka su ka nemi a dauki mataki.

KU KARANTA: Duk da na fadi amma zan yi kokarin ganin Buhari ya zarce inji Ambode

Mista Adefuye yace ko da su ka kira Gwamna Ambode a waya domin su nuna masa inda baraka ta ke, sai su ka ga ba ya daukar wayan su. Adefuye yace sun nemi Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya sa baki a rikicin Gwamnan da Tinubu.

Anthony Adefuye yace ya tashi tare da wani babban ‘Dan APC a Legas Alhaji Tajudeen Olusi su ka samu Tinubu domin jin abin da yake faruwa a lokacin tsakanin sa da Gwamna Ambode amma sai su ka ji dai Gwamnan shi ma bai daukar wayan sa.

A karshe dai bayan duk sun yi abin da za su iya dole aka saduda inji Jigon na APC. Adefuye yace ana ji ana gani Gwamna mai-ci Akinwunmi Ambode ya sha kasa Babajide Sanwo-Olu wajen wanda Bola Tinubu ya tsaida.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel