Ganduje ya amince da kashe makudan miliyoyi domin wasu muhimman aiyuka a Kano

Ganduje ya amince da kashe makudan miliyoyi domin wasu muhimman aiyuka a Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe miliyan N514 domin samarwa tare da kafa wasu na'urorin taransifoma domin inganta samar da wuta

- Garba ya kara da cewa majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da kashe biliyan N1.3 domin gyaran wasu muhimman hanyoyi da ke cikin birnin Kano

- Naira miliyan N5m gwamnati ta ware a matsayin diyya ga iyalin wani mutum da jami'in KAROTA ya yi sanadin mutuwar sa," a cewar Garba

Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe miliyan N514 domin samarwa tare da kafa wasu na'urorin taransifoma domin inganta samar da wutar a birni da kauyukan jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ne ya sanar da hakan a yau, Alhamis.

Garba ya kara da cewa majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da kashe biliyan N1.3 domin gyaran wasu muhimman hanyoyi da ke cikin birnin Kano.

Ya kara da cewar an bawa ma'aikatar kudi umarnin fitar da kashi 30% na kundin ga 'yan kwangila 8 domin su fara aikin gyaran hanyoyin.

Ganduje ya amince da kashe makudan miliyoyi domin wasu muhimman aiyuka a Kano

Ganduje
Source: Depositphotos

Daga cikin hanyoyin da za a gyara akwai titin Obasanjo, titin 'Yan tsaki a Tudun Murtala, titin Manladan a unguwar Kulkul, titin Sheikh Jafar, da wasu da dama, a cewar Garba.

Sannan ya kara da cewar gwamnati ta amince da fitar da miliyan N31.8m domin ciyar da daliban da ke karatu a makarantun Shehu Minjibir, Musa Saleh Kwankwaso Boarding Primary School da gidan marayu na Mariri.

DUBA WANNAN: Zabe maye gurbi a jihohin arewa 3: INEC ta fitar da sunayen 'yan takara da jam'iyyun su

"Naira miliyan N5m gwamnati ta ware a matsayin diyya ga iyalin wani mutum da jami'in KAROTA ya yi sanadin mutuwar sa," a cewar Garba.

Kazalika ya bayyana cewar an ware miliyan N11.5 domin yasar magudanan ruwa da ke unguwannin Daneji da Sheshe a cikin birnin Kano.

Kwamishinan ya jaddada aniyar gwamnatin jihar Kano na cigaba da shimfida aiyukan a jihar Kano da kuma inganta walwalar jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel