Ya kashe matar sa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya

Ya kashe matar sa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya

Jami'an 'yan sanda na kasar Rasha sun kama wani mutum mai suna Oleg Kirkunov mai shekaru 54 bisa laifin kashe matarsa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya a wani dakin baki da ke gidansa.

Kirkunov ya shaidawa 'yan sanda cewa yayansa, Evgeny ya kawo masa ziyara ne a gidansa inda suka ci abinci tare a birnin Ufa da ke Rasha.

Bayan sun gama cin abincin ne shi da matarsa Sukhanova suka amince Evgeny ya kwana a gidan kuma suka bashi makullin dakin baki domin ya kwanta kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Ya kashe matar sa da kaninsa bayan ya kama su turmi da tabarya

Ya kashe matar sa da kaninsa bayan ya kama su turmi da tabarya
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: 'Yan kasuwa sun yiwa El-Rufai ihu, sunyi watsi da tayin da ya yi musu

Oleg ya farka cikin dare saboda wani hayaniya da ya rika ji kuma a lokacin ne ya kura cewar matarsa ba ta kwance a gadonsu na aure.

Hakan ya sa ta tashi domin ya dubo matarsa kuma ya bincika mene hayaniyar da ya ke ji kwatsam sai ya ga yayansa da matansa suna saduwa a dakin baki.

Oleg wanda dama dan farauta ne ya yi maza ya dako bindigarsa ya harbe matarsa a yayin da ta ke kwance a kan gado, sannan ya juya ya harbe yayansa a lokacin yana kokarin sanya kaya kafin ya tsere.

A nan take ya yiwa 'yan sanda waya ya kuma fada musu cewar shine ya kashe yayansa da matarsa tare da fada musu dalilin da yasa ya aikata hakan.

Hukumar bincike na kasar Rasha ta tabbatar da afkuwar wannan lamarin inda ta ce ana tsare da mai laifin kuma ana tuhumarsa da laifin kisan mutane biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel