Shugaba Buhari ya karbi bakuncin wasu sanatocin APC (Hotuna)
A jiya, Litinin 5 ga watan Nuwamba ne shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wasu daga cikin sanatocin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a gidan gwamnati da ke babban birnin tarayya Abuja.
Baya ga sanatocin akwai wasu ministocin shugaba Muhammadu Buhari da suka samu hallartar taron domin taya shugaban kasar tarbar bakinsa.
Wasu daga cikin wadanda suka hallarci taron sun hada da Sanata Abdullahi Abubakar Gumel, Sanata Sani Mustapha, Sanata Olanrewaju Tejuosho, Sanata Ahmed Lawan, Senator Gbenga Ashafa, Senator Ibrahim Umar Kurfi da kuma dan majalisa, Hon Farouk Aliyu
Ministocin da suka hallarci taron sune Ministan Sufurin jiragen Sama, Hadi Sirika da Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Sanatoci sunyi amai sun lashe a kan amincewa da bukatar Buhari

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Sai dai a lokacin wallafa wannan rahoton ba a tabbatar da dalilin da yasa Sanatocin suka kaiwa shugaban kasar ziyara ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng