El-Rufai ya canjawa wani babban sarki a Kaduna suna bayan ya mayar da shi sarkin yanka
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya amince da yiwa Mai Martaba Dr. Danjuma Barde (Esu Chikun) wanda a baya akafi sani da Sa Gbagyi karin girma zuwa sarki mai daraja ta daya.
An fara yiwa Sa Gbagyi nadin sarauta ne a ranar 29 ga watan Disamban 2000 sannan ya kara aiki a ranar 18 ga watan Janairun 2001 a matsayin sarki mai daraja ta uku. An yi masa karin girma zuwa sarki mai daraja na biyu a shekarar 2007.
Sanarwan karin girmar da gwamnan ya yi masa yana dauke ne cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun gwamnan jihar, Samuel Aruwan a yau ranar Litinin.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: Fallasa: An gano yadda gwamnatin Buhari ta waske da N378bn
A yayin da ya ke taya shi murna, El-Rufai ya ce, "Mai martaba Dr. barde ya cacanci karin karamcin da aka yi masa saboda irin gagarumar gudunmawar da ya ke bayarwa wajen zaman lalfiya."
Gwamnatin jihar ta amince da yiwa masarautar Chikun karin daraja ne bayan Ma'aikatar Harkokin Kananan Hukumomi karkashin kwamshinanta, Farfesa Kabir Mato da saka hannu kan takardan karin darajar saboda irin gudunawar da Dr. Barde ya ke bayarwa wajen hada kan al'umma da zaman lafiya.
An canja sunan masarautar ne daga Gbayi zuwa Chikun saboda cewar ba sarautar wata kabila bace amma dukkan mutanen da ke karkashin masarautar na Chikun.
Mai martarba Dr. Barde yana da digiri a fannin koyarwa kuma ya yi aiki a matsayin malamin makaranta sannan ya zama babban jami'in ilimi a jihar. Dr Barde kuma tsohon dan majalisar jihar Kaduna ne.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng