Matan Kaduna sun amince da wanda El-Rufai ya dauka a matsayin Mataimakiyar sa
– Kungiyar wasu Mata a Kaduna sun yabawa matakin da El-Rufai ya dauka
– Gwamna El-Rufai ya zabi mace tayi takara da shi a zabe mai zuwa na 2019

Asali: UGC
Mun samu labari daga gidan yada labarai na BBC Hausa cewa wasu Kungiyoyin da ke Jihar Kaduna sun nuna cewa sun yi na’am da matakin da Gwamna Nasir El-Rufai ya dauka na zaben mace a matsayin Abokiyar Takarar sa a 2019.
Wasu gungun Mata da ke Jihar Kaduna sun nuna cewa zabin da Gwamna Nasir El-Rufai yayi na daukan mace a matsayin Abokiyar takarar sa a zabe mai zuwa na 2019. Gwamnan ya dauki Hadiza Balarabe ne tayi masa Mataimakiya a APC.
KU KARANTA: 2019: Mataimakin Gwamnan Kaduna zai yi takarar Sanata
Matan da ke Jihar sun bayyanawa BBC Hausa cewa dauko mace da aka yi a matsayin ‘Yar takara yayi masu dadi kwarai. A cewar wadannan Mata, an dade ana barin Mata su na wahala duk da irin gudumuwar da su ke badawa.
Hajiya Hadiza Balarabe ce ke rike da Hukumar kula da lafiya na Jihar Kaduna inda Gwamnan yace ta kawo wasu gyare-gyare da sauye-sauye da su ka habaka tsarin kiwon lafiya a matakin farko na Jihar Kaduna a Gwamnatin nan ta APC.
Sai dai kuma wasu mutane su na sukar wannan mataki da Gwamnan ya dauka ganin cewa Hadiza Balarabe Musulma ce. Wannan ne dai kusan karon farko da Musulmai biyu za su yi takarar Gwamna a Jihar Kaduna mai dauke da Kiristoci.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng