Manyan ayyukan cigaba guda 4 da jahar Zamfara ta amfana dasu daga gwamnatin tarayya

Manyan ayyukan cigaba guda 4 da jahar Zamfara ta amfana dasu daga gwamnatin tarayya

A yayin da kakar zaben shekarar 2019 ke kara kartowa, yan siyasa na cigaba da kokarin ganin kodai sun zarce a kujerun da suka yi dare dare akai, ko kuma kokarin ganin dan gidansu ko kuma duk wanda suka tsayar takara ya kai labari.

Haka zalika wasu yan siyasan na tuna ma jama’ansu alkawurran da suka yi musu kuma suka cika musu, domin da haka ne kadai jama’a masu zabe zasu auna kokarin da dan siyasan ya yi, sai su yanke hukuncin cancantarsa ko akasin haka.

KU KARANTA: Take hakkokin bil adama: Majalisar dinkin Duniya ta fara binciken kasashe 14, har da Najeriya

Da wannan ne Legit.com ta binciko wasu manyan ayyukan cigaba da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya dare mukamin bayan samun nasara a zaben shekarar 2015.

Manyan ayyukan cigaba guda 4 da jahar Zamfara ta amfana dasu daga gwamnatin tarayya
Zamfara
Asali: Facebook

An sha mamaki a yayin wannan zabe dai, inda dan adawa Buhari ya kayar da shugaba mai ci, shugaban kasa Goodluck Jonathan, inda Buhari ya samu kuri’u sama da miliyan goma sha biyar yayin da Jonathan ya samu kuri’u miliyan goma sha biyu da yan kai.

Al’ummar jahar Zamafar ma ba’a barsu a baya ba wajen kada ma Buhari kuri’u, inda bayan kammala zaben hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanar da Buhari ya samu kuri’u dubu dari shida da goma sha biyu, da dari biyu da biyu (612, 202).

A sakamakon gudunmuwar da jama’an jahar suka baiwa Buhari, babu yadda za’ayi ya manta dasu, don haka ga wasu daga cikin muhimman ayyukan cigaba da Buharin ya yi a Zamfara:

- Aikin gina babbar hanyar Kasuwar Daji-Gusau

- Aikin gina gidaje don amfanin jama’a

- Daukan matasa 32, 186 a karkashin tsarin N-Power

- Aikin tabbatar da tsaro na operation sharan daji

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng