Dakarun ‘Civilian JTF’ sun yi ma yan ta’addan Boko Haram kisan gilla a jahar Borno

Dakarun ‘Civilian JTF’ sun yi ma yan ta’addan Boko Haram kisan gilla a jahar Borno

Har yanzu dai ana cigaba da fafatawa a yakin da ake yi tsakanin mayakan kungiyar ta’addanci Boko Haram da jami’an hukumomin tsaron Najeriya, kai har ma da sauran jama’an gari, tunda dai yan ta’addan ba wai sun daga musu kafa bane.

Sai dai daga cikin jama’an garin dake yaki da mayakan Boko Haram akwai wasu jaruman matasa kuma jajirtattu da ake yi ma lakabi da suna ‘Civilian JTF’ watau dakarun fararen hula, wadanda suke taimaka a Sojoji da ilimin da suke da shi na lunguna da sakon jahar Borno da ma dajin Sambisa.

KU KARANTA: Karanta wasu muhimman bayanai 10 game da Hadiza sabuwar mataimakiyar Gwamna El-Rufai

Dakarun ‘Civilian JTF’ sun yi ma yan ta’addan Boko Haram kisan gilla a jahar Borno
Dakarun ‘Civilian JTF’
Asali: UGC

Da haka ne sau dayawa Sojoji tare da hadin gwiwar Civilina JTF suke kai ma mayakan Boko Haram farmaki, tunda suma suna da kananan makamai, motocin zirga zirga da kuma layoyi da dai sauran duk wani abu da zai taimaka musu a harkar da suka sanya a gaba.

A irin haka ne aka yi wata artabu tsakanin matasan da mayakan Boko Haram a kauyen Gazabure, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito, inda a wannan hari an yi dauki ba dadi, wanda ya baiwa matasan nasarar kashe mayakan Boko Haram fiye da goma.

Majiyar Legit.com ta ruwaito an yi wannan kashe kashe ne a kauyen Gazabure dake cikin karamar hukumar Gubio na jahar Borno ne, inda rahotanni suka tabbatar da cewa matasan civilian JTF ne suka kai samamen akan yan Boko Haram, suka kuma yi nasara.

Bugu da kari jaruman matasan sun daddaure gawarwakin yan ta’addan a jikin motarsu domin su bayyana ma jama’a don ya zama shaida, da kuma don ya zama izina ga sauran yan ta’addan da cewa wannan shine makomarsu idan har basu daina abinda suke yi ba.

A yan kwanakin baya ma an samu hare haren mayakan Boko Haram a wasu kauyuka dake cikin karamar hukumar Konduga, inda suka kone gidaje da dama, tare da kashe mutanen kauyukan, daga ciki har da wani limamin masallaci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel