Ku daina yaudarar jama'a da gan-gan - Buhari ga 'yan bokon Najerya
- Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi 'yan Boko su dena yada kalaman da ka iya harzuka al'umma ko raba kansu
- Shugaban kasa ya bayyana cewa gwamnati za ta hukunta duk wanda aka samu yana yada kiyaya
- Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnati za tayi iya kokarinta wajen kare lafiya da dukiyoyin al'umma
Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi 'yan Bokon Najeriya su dena rudar al'ummar Najeriya ta hanyar furta kalamai da ka iya tada zaune tsaye.
Shugaban kasan ya yi wannan gargadin ne a jawabinsa yayin yaye daliban jami'ar Uyo karo na 24 da aka gudanar a harabar jami'ar a yau Asabar.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Ni ne na kafa APC, ba kuma zan fita daga cikinta ba - Gwamnan jam'iyyar
Shugaban kasan wanda ya samu wakilcin Mr Ibrahim Yakasai, Direktan Yada Labarai na Cibiyar Kula da Jami'o'in Najeriya (NUC) ya ce babu yadda za a samu cigaba a kasa idan akwai kiyaya tsakanin al'umma.
Ya ce jami'o'i wuri ne da ake bawa manyan gobe tarbiya da koyar da su tunani saboda haka ya kamata al'ummar Najeriya su rika koyon darrusa na gari daga wajen 'yan bokon musamman yanzu da ake tunkarar zaben 2019.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta dauki mataki kan duk wata kungiya ko mutum da aka samu yana yadda kalaman firgita mutane ko kuma yada kiyaya da gaba tsakaninsu.
Shugaba Buhari ya ce gwamnatin tarayya za tayi iya kokarinta domin ganin cewar ta tabbatar da zaman lafiya da kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng