Matasan Arewa sun goyi bayan Atiku a kan kudirinsa na rage farashin man fetur

Matasan Arewa sun goyi bayan Atiku a kan kudirinsa na rage farashin man fetur

- Shugaban kungiyar AYCF, Yerima Shettima ya yaba wa Atiku kan alkawarin da ya yi na rage kudin man fetur inda ya zama shugaban kasa

- Yerima ya yi ikirarin cewar jam'iyyar APC ta jefa al'ummar Najeriya cikin tsanani da wahalhalun rayuwa

- Yerima ya yi alkawarin wayar da kan matasan arewa domin su zabi jam'iyyar PDP a babban zaben 2019

Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta yi kira ga dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar ya mayar da hankali kan yakin neman zabensa, ya yi watsi da sukar da 'yan adawa ke masa.

Shugaban kungiyar na kasa, Yerima Shettima ne ya yi wannan kirar yayin da ya ke hira da manema labarai a Kaduna inda ya kara da cewa Atiku dan takara ne mai al'umma kuma ya fara bulo da hanyoyin da zai magance matsalolin Najeriya.

Matasan Arewa sun goyi bayan Atiku kan wata muhimmiyar batu
Matasan Arewa sun goyi bayan Atiku kan wata muhimmiyar batu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ni ne na kafa APC, ba kuma zan fita daga cikinta ba - Gwamnan jam'iyyar

Ya bayyana cewar niyyar da Atiku ke da shi na rage kudin man fetur da iskar gas tsari ne mai kyau da zai rage radadin talauci da wahalhalun rayuwa da talaka ke fama da shi.

"Muna goyon bayan duk wanda zai rage wa talakan Najeriya tsadar rayuwa kuma muna masa addu'an samun nasara,"

" Dukkan wadanda ke sukan Atiku suna kokarin kawar da hankalin al'umma ne daga yadda lamura suka tabarbare karkashin mulkin APC tun daga matakin tarayya har zuwa jiha da kananan hukumomi," inji Shettima.

Alhaji Shettima kuma ya tabbatar wa tsohon mataimakin shugaban kasar cewa zai tattaro wa PDP kuri'un matasan arewa domin ganin ya yi nasara a babban zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164