Tazarcen Buhari 2019: Wa zai fi moras wannan lamari tsakanin Igbo da Yoruba?

Tazarcen Buhari 2019: Wa zai fi moras wannan lamari tsakanin Igbo da Yoruba?

- Alheri danko ne inji hausawa

- Amma kuma wani lokaci ba a sa ran kura zata rama aniyar ta

- Zaben Buhari a 2019 na nufin komawar mulki kudu maso yamma a 2023

Wannan Ra'ayin marubuchiya ne, na siyasa: Buchi Obuchi

Tazarcen Buhari 2019: Wa zai fi moras wannan lamari tsakanin Igbo da Yoruba?
Tazarcen Buhari 2019: Wa zai fi moras wannan lamari tsakanin Igbo da Yoruba?
Asali: UGC

Hausawa dai na cewa alheri danko ne, ka yadda shi a nan, ka tsince shi a gaba.

A lissafin da siyasar Najeriya ke ciki, Idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma mulki a 2019,zuwa 2023 sai mulki ya koma kudu maso gabas.

Kwatsam! Babatunde Fashola, Ministan wuta, aiyuka da gidaje ya karyata wannan hasashen.

A jawabin da yayi a wani taro akan ababen more rayuwa, Ministan na cewa : Kun san shugabanci zai koma kudu maso yamma ne bayan kun zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019? Kuri'ar ku ga Buhari na nufin komawar shugabanci kudu maso yamma ne a 2023. Na tabbatar zaku yi abinda ya dace. "

DUBA WANNAN: An roki NLC ta ajje yajin aikin talata

Abin ya ruda lissafi, shin nasarar Buhari a 2019 ba tana nufin nasarar komawa mulki ga kudu maso gabas bane? Ya za'a ce kudu maso yamma da suka mulki kasar na shekara 8 su koma cikin lissafin? Meke faruwa ne?

Bayan zurfin tunani akan subul da bakan da Fashola yayi, sai muka gano cewa Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kawai ta kanta take yi.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng