Bana an sami damina mai albarka, don haka abinci zai sauko - Gwamnati

Bana an sami damina mai albarka, don haka abinci zai sauko - Gwamnati

- Noma da kiwo ya zamo abin dogaro ga mutanen Najeriya

- Amma kuma fari ko ambaliyar ruwa sun zamo barazana a yan shekarun nan

- Dumamar yanayi ma yakan kawo gudummawa ga yanayi

Bana an sami damina mai albarka, don haka abinci zai sauko - Gwamnati
Bana an sami damina mai albarka, don haka abinci zai sauko - Gwamnati
Asali: Depositphotos

Noma da kiwo jigo ne gurin samar da madogar ga mutanen Najeriya. Amma kuma ambaliyar ruwa ko fari sun zamo barazana a yan shekarun nan. Wanda hakan kan kawo asara a yankunan kasar nan.

Dumamar yanayi ma barazana ce da take kawo canje canje. Daya daga cikin jigon yanayi kuwa shine ruwan sama. Idan aka samu canji a yanayin ruwan sama, akan samu canji a fannin noma a duk duniya.

Abin farincikin shine, karuwar ruwan sama da aka samu a 2018 a Najeriya, ya zamo alheri ga noma. A takaice dai Najeriya ta samu karuwa ta fannin noma da kiwo fiye da a 2017.

DUBA WANNAN: An roki NLC ta ajje yajin aikin talata

Wannan binciken anyi shi ne a cibiyar bincike da bunkasa aiyukan noma NAERLS da hadin guiwar ma'aikatar noma da bunkasa karkara ta Gwamnatin tarayya.

Daraktan NAERLS, Farfesa Mohammed Othman ne ya bayyana hakan.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng