Yajin aiki Nov. 6th: An roki 'yan kwadago dasu hakura da tafiya yaji, kan N30,000
- BMO tayi kira ga NLC data jinginar da batun tafiya yajin aiki
- Ya kamata suyi duba ga mutanen Najeriya akan wannan batu
- Ya kamata NLC su zauna da gwamnati a teburin sulhu

Asali: UGC
Hadaddiyar kungiyar watsa labarai ta Buhari BMO tayi kira ga NLC data jinginar da batun tafiya yajin aiki.
Da suke tattaunawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja kungiyar tace ya kamata NLC ta zauna da gwamnati a bisa wannan kudiri nata na neman karin albashi.
Kungiyar tayi kira ga NLC da tayi duba ga ra'ayin al'ummar Najeriya wadanda zasu sha wahala idan aka tafi wannan yajin aiki,inda ya basu shawara dasu dawo teburin sulhu.
DUBA: Wadanda Buhari ya biya fansho
Wannan yajin aiki ba ma'aikata kadai zai shafa ba zai shafi gwamnati da kuma daukacin al'ummar kasar nan.
Kungiyar ta kara da cewa gwamnatin Buhari tana tafiya ne bisa jindadin al'umma sannan zatayi iyakar kokarin ta wajen ganin sun samu rayuwa mai inganci.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng