Rikicin Kaduna: An gurfanar da mutane 97 a gaban kotu
A yau, Alhamis, ne kwamishinan 'yan sanda a jihar Kaduna, Malam Ahmad Abdurrahaman, ya sanar da cewar hukumar 'yan sanda ta gurfanar da mutane 97 a gaban kotu bisa zarginsu da hannu a rikicin jihar Kaduna.
Abdurrahaman ya bayyana hakan ne yau a Kaduna yayin ganawa da manema labarai tare da sanar da cewar an gurfanar da mutanen ne a kotun majistare da ke titin Ibrahim Taiwo a ranar 24 ga watan Oktoba.
"Mun kara gurfanar da karin wasu mutane 52 a jiya, Laraba, 31 ga watan Oktoba," in ji kwamishinan.
Kazalika ya kara da cewar tuni zaman lafiya ya dawo a duk yankin da rikicin ya shafa kuma jama'a sun koma bakin harkokinsu.

Asali: Original
Abdurrahaman ya kara jadda kudurin hukumar 'yan sanda na cigaba da kokarin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa tare da yin kira ga jama'a su bawa jami'an hukumar 'yan sanda hadin kai ta hanyar bayar da bayanai a kan batagari.
DUBA WANNAN: Ku bar garinku tun kafin mu dirar ma ku - 'Yan bindiga sun bawa jama'a a Katsina wa'adin
Kwamishinan ya ce ko a cikin satin sati biyu da su ka wuce, hukumar 'yan sanda ta kara kama wasu mutane 26 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
Sannan ya sanar da cewar 'yan sanda sun yi nasarar kama wasu makamai da su ka hada da wata bindiga piston kirar gida, bindigar baushe daya, alburusai, bindigar bogi ta katako, wukake, tabar wiwi da sauran su.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng