'Yan Bindiga sun yi garkuwa da Ma'aikatan Lafiya 3 a jihar Nasarawa

'Yan Bindiga sun yi garkuwa da Ma'aikatan Lafiya 3 a jihar Nasarawa

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu 'yan ta'adda rike da bindigu suka yi garkuwa da wasu kananan ma'aikatan kiwon lafiya 3 a babbar hanyar jihar Nasarawa zuwa garin Toto.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Mista Kennedy Idrisu, shine ya bayar da tabbacin wannan mummunan lamari da ya bayyana cewa ya auku ne yayin da Ma'aikatan ke kan hanyarsu ta zuwa kauyen Bugan-Gwari inda maharan suka katse ma su hanzari.

Wannan mummunan lamari ya auku da misalin karfe 12.00 na rana inda 'yan ta'adda rike da bindigu suka datse hanyar Ma'aikatan na lafiya dake kan hanyarsu cikin wata babbar Mota kirar Toyota Hilux.

'Yan Bindiga sun yi garkuwa da Ma'aikatan Lafiya 3 a jihar Nasarawa
'Yan Bindiga sun yi garkuwa da Ma'aikatan Lafiya 3 a jihar Nasarawa
Asali: Facebook

Kamar yadda babban jami'in na 'yan sanda ya bayyana, tsausayi da Hausawa kan ce ba ya wuce ranarsa ya ritsa da Ma'aikatan na Lafiya yayin da suke kan hanyarsu ta gudanar da aikin duba gari daga birnin Lafia zuwa kauyen Gadabuke dake karamar hukumar Toto a jihar ta Nasarawa.

KARANTA KUMA: An yi karar shugaba Buhari da Gwamnoni 36 na Najeriya kan mafi karancin Albashin Ma'aikata

Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu hukumar 'yan sanda reshen jihar ta bazama wajen gudanar da binciken diddigi domin ceto Ma'aikatan daga hannun wannan miyagu yayin da suke ci gaba da zama cikin shirin ko ta kwana sakamakon aukuwar ta'addancin fashi da makami da ya yi kamari a yankin.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani babban jami'in sojin ruwa mai suna Omoniyi Kola a yankin Sapele na jihar Delta inda suke neman fansar N4m kafin ya samu wani 'yanci da walwala.

Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng