Masu zafin kishin Islama a Pakistan na neman sai an kashe musu wata baiwar Allah, ko me tayi?
- Ance Asia Bibi ta zagi annabi ne a 2010
- Ta karyata hakan, an kulle ta shekaru 10
- Kotu ta sake ta, amma sunce sai an kashe musu ita

Asali: Facebook
Kasar Pakistan na cikin yanayin ha'ula'i, yayin da komai ya tsaya cik, saboda kokarin masu zafin kishin Islama, wadanda sun kai 3m a kasar, suke so sai lallai gwamnati ta kashe musu, ko kuma ta basu damar kashe wata mata kirista.

Asali: Facebook
A 2010 ne aka zargi Asia Bibi, mace mai yara hudu, da jika daya, da laifin wai ta zagi addinin Islama da ma Annabin addinin, duk da ita kirista ce.

Asali: Twitter
An kama ta an kulle shekaru 10, daga baya kuma aka yanke mata hukuncin kisa kan wai wannan laifi. Kasashen duniya sun koka, amma Pakistan na tsoron tashin-tashina.

Asali: Twitter
A yanzu dai kotun koli tace a saki wannan baiwar Allah ta koma gida, musamman ganin ita ma 'yar Pakistan ce, lamari da ya harzuka masu zafin kishin addinin Islama.
Sun fito kwansu da kwarkwatarsu kan lallai sai sun kashe ta, muddin har dai aka barta ta koma gida, lamari da ka iya yiwuwa tunda du din dubbai ne.
DUBA WANNAN: An kira Ganduje Majalisa gobe
Shugaban Kasar, Imran Khan, yayi Allah wadai da masu kishin, wadanda ake sa rai gobe juma'a ma abin sai ya fi hakan qazanta.
An sha kashe masu irin wannan laifi a Pakistan, kuma da yawa daga wadannan masu zafin ra'ayi, suna da alaka da ta'addancin Taliban a Afghanistan da Pakistan din.
A addinin Islama dai, kisan ne ke kan duk wanda ya bar addinin, ko kuma ya zagi addinin, ko kuma ya kushe shariar addinin.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng