Siyasar Kano: An kira gwamna Ganduje majalisa, ko anzo fadan karshe ne?

Siyasar Kano: An kira gwamna Ganduje majalisa, ko anzo fadan karshe ne?

- Kwamitin da aka kafa akan binciken gwamnan jahar Kano ta nemi ya gabatar da kanshi a gareta

- A satin daya gabata shugaban jaridan Daily Nigerian yan gurfana a gaban kwamitin

- An bawa gwamnan damar daukar Lauya

Siyasar Kano: An kira gwamna Ganduje majalisa, ko anzo fadan karshe ne?
Siyasar Kano: An kira gwamna Ganduje majalisa, ko anzo fadan karshe ne?
Asali: Twitter

Majalisar jihar Kano, karkashin kwamiti da ta kafa na bincike kan zargin da ake wa Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje da karbar cin hanci ta nemi da ya gabatar da ansa a gabanta a ranar Juma'a watau gobe kenan.

Kwamitin ya bawa gwamnan damar daukan lauya idan ya so.

Kwamitin yace an turawa gwamnan bidiyo a lokacin da yake karbar cin hanci na daloli.

Bidiyo na uku da aka saka a jiya ya nuna gwamnan a lokacin da yake karbar cin hanci na daloli yana sanye da bakin kaftani.

Gwamnan ya musanta wannan batu inda yace shiri ne.

DUBA WANNAN: Saura wata uku zabe, ga iya shirin INEC

A satin daya gabata mai jaridar Daily Nagerian Jaafar Jaafar ya gabatar da kansa gaban kwamitin inda ya nuna wasu bidiyon dake nuna gwamnan yana karbar kudin.

Bayan bayyana bidiyo na uku kwamitin ya nemi gwamnan daya gaggauta bayyana a gabanta a ranar Juma'a wanda ciyaman na kwamitin Alhaji Baffa Babba Dan'agundi ya rattaba hannu akai.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng