2019: Jam’iyyar PRP tana karfi a Jihar Kano bayan shigowar Takai

2019: Jam’iyyar PRP tana karfi a Jihar Kano bayan shigowar Takai

Labari yana zuwa mana daga TTV network cewa Jam’iyyar adawa ta PRP tana cigaba da kara karfi a Arewacin Najeriya musamman a Jihar Kano tun bayan da Salihu Sagir Takai ya fice daga PDP ya koma Jam’iyyar.

2019: Jam’iyyar PRP tana karfi a Jihar Kano bayan shigowar Takai
Salihu Takai ya fara janyewa Jam’iyyar PDP Jama’a a Kano
Asali: Twitter

Hon. Muhammad Aminu wanda aka fi sani Abba Boss kuma yana cikin manyan ‘Yan Kwankwasiyya a Jihar Kano ya koma Jam’iyyar PRP. Abba Boss Gama ya bi tafiyar Malam Salihu S. Takai wanda ya bar PDP kwanan nan.

Haka kuma mun samu labari cewa Injiniya Abdullahi Garba Ramat wanda Jam’iyyar PDP ta ba tutar takarar Majalisar Tarayya a Mazabar Minjibir da Ungogo yayi watsi da takarar ya sauya-sheka zuwa Jam’iyyar ta PRP.

KU KARANTA: Sanata Shehu Sani ya koma jam’iyyar PRP bayan ya bar APC

Dr. Ibrahim Muazzam Maibushira wanda ya taba rike Shugaban Kungiyar Hisbah a Jihar Kano yana cikin wadanda su ka koma Jam’iyyar PRP kamar yadda mu ka ji. Maibushira ya taba neman Sanatan Kano a Jam’iyyar ANPP.

A jiya kun ji labari cewa tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafeez Abubakar ya fice daga Jam’iyyar adawa ta PDP inda ake sa rai zai koma Jam’iyyar ta PRP tare da Salihu Sagir Takai wanda PDP ta hana tikitin takara.

Kun san cewa Salihu Takai wanda yana cikin manyan ‘Yan takarar Gwamnan Jihar Kano ya bar PDP ne a sakamakon tsaida Surukin tsohon Gwamnan Jihar Kano Abba Yusuf da aka yi a matsayin ‘Dan takara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel