Babbar Magana: Kotu ta amince da tuhumar gwamnan APC a kan karyar takardun karatu

Babbar Magana: Kotu ta amince da tuhumar gwamnan APC a kan karyar takardun karatu

- Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta amince da gaggauta fara sauraron karar da aka shigar da gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow

- Kungiyar 'Incorprated Trustees Of Global Integrity Crusade Network' ce ta shigar da karar gwamnan bisa zarginsa da badakalar takardar karatun sakandire

- Bayan shigar da korafi a gaban kotun ranar 22 ga watan Oktoba, jastis Quadri ya amince da bukatar ma su kara na gaggauta fara sauraron karar

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya, karkashin mai sharia Jastis B. O. Quadri, da ke Abuja ta amince da gaggauta fara sauraron karar da aka shigar da gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, bisa zarginsa da yin amfani da takardun kammala makarantar sakandire na bogi.

Kungiyar 'Incorprated Trustees Of Global Integrity Crusade Network' ce ta shigar da karar gwamna Bindo na Adamawa a kan zarginsa da badakalar takardun kammala makarantar sakandire.

Babbar Magana: Kotu ta amince da tuhumar gwamnan APC a kan karyar takardun karatu
Jibrilla Bindo
Asali: Facebook

Daga cikin wadanda kungiyar ta hada a takardar da ta shigar da kara gaban kotun akwai hukumar tsara jarrabawar kammala makarantar sakandire na kasashen Afrika ta yamma (WAEC), hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), jam'iyyar APC, da kuma hukumar 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Kisan dan sanda: An kama tsohon shugaban majalisa da wasu 49

Bayan shigar da korafi a gaban kotun ranar 22 ga watan Oktoba, jastis Quadri ya amince da bukatar ma su kara na gaggauta fara sauraron karar tare da aika sammaci ga gwamna Bindo da kuma ofishin WAEC da ke Adamawa da Legas.

Jstis Quadri ya amincewa kungiyar ta mika takardar sammaci ga gwamna Bindo hannu da hannu ko kuma ta aika masa da sakon takardar ta hannun kamfanin aika kaya na DHL.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng