Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Abuja

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Abuja

Rahoton da muka samu daga Channels tv ya bayyan cewa shuguba Muhamadu Buhari ya koma gida babban birnin tarayya Abuja bayan ziyarar da ya kai jihar Kaduna a safiyar yau.

Shugaban kasan ya kai ziyarar ne saboda ganawa da Sarakuna da shugabanin addinai da ke jihar kan barkewan rikice-rikice a jihar ta suka rika faruwa a cikin makon da ya gabata.

Shugaba Buhari ya gana da masu ruwa da tsaki da wadanda rikicin ya shafe su a dakin taro na Umaru Musa Yar adua da ke Murtala Square a Kaduna.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Abuja
Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo Abuja
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Karin bayani kan gawar Janar Alkali da aka kashe a Dura-Du a Jos

Buhari ya gana da shugabanin kungiyar Jama'atul Nasril Islam (JNI) da Christian Association of Nigeria (CAN) inda ya tabbatar musu cewa gwamnatin tarayya za ta dauki tsatsauran mataki ne hukunta dukkan wadanda aka samu hannu cikin rikicin.

Bayan mika ta'aziyarsa da iyalan wadanda suka rasu, shugaban kasan ya shawarci al'ummar jihar su zauna lafiya da juna kana ya bukaci a cigaba da bincike tare da tabbatar da cewa an hukunta wadanda aka samu da hannu cikin rikicin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164