Hanyoyin maganin kisan gilla da ake yiwa 'yan shi'a a kasar nan
Dawajewa: Wannan rubutu ra'ayin marubuci ne, ba na Legit.ng ko sauran ma'aikatanta ba
- 'Yan shia na kamanceceniya da Boko Haram ta bangarori da dama
- Da yawansu, basu zuwa makaranta sai kukan suna son shahada
- Gwamnatin Tarayya ta rasa yadda zata yi dasu

Asali: Twitter
Tun bayan da aka gano aniyar 'yan Boko Haram ta sai lallai sun kore gwamnatin Najeriya sun kafa ta shariar Islama ake kaffa-kaffa dasu, ana dan tauna wa ana hurawa, basu ji ba, basu daina ba, domin sun raina hukuma, kamar yadda malaminsu Muhammad Yusuf ya koya musu.
Yanzu dai an shekara 10 kenan ana yakar su ana kashe su, sun ki karewa, basu fi su 10,000 ba a kiyasin gwamnati.
'Yan shi'a a Najeriya, daga 1980 zuwa yau, kun doshi miliyoyi, suma kuma malami daya suke bi tal, wadda hakan babbar matsala ce dama.
Kamar 'yan Boko Haram, 'yan shi'a sunce allan katafar babu wata gwamnati da zasu girmama sai ta Allah, wadda limaminta tilo yake can Iran, wanda kuma shi kadai ne zai ce suyi ko su bari, sabanin dokokin Najeriya.
DUBA WANNAN: An sami Pasto da ke so a cire masa kudi daga albashin mutane ta dole
Tun zamanin mulkin soja, aka farga da mummunar akida da El-Zazzaki yake yada wa, ta ya kiar da gwamnatin da ba ta Allah ba, ya kawo tasu ta Sharia tsarin Shia, kamar yadda aka yi a Iran a 1979.
Tuni Larabawa suka daqile irin wadannan shirye shirye a Misra, Yaman, Labanon, da Iraqi, duk da daga baya, Shiar ta zagayo ta kwaci Labanon, inda har mayakanta karkashin Hasan Nasralla suka sami makamai da sunfi na gwamnatin kasar karfi.
Yanzu kam, sai aka fara gani Iran ma tana aikoo da makamai Najeriya, inda a 2010, aka kama sinqi sinqi na makamai irin haka a Legas, lokacin mulkin Jonathan da Ahmedinajad, lamari da ba'a iya daukar mataki a kai ba saboda sakaci.
Shugaban Iran ya zo Najeriya har Abuja daga baya, amma ba wurin gwamnati yazo ba, a'a, wurin yaran da suke kafawa a Najeriya yazo, ya kuma gana dasu, ya tafi.
Rigimar yankin gabas ta tsakiya bata shafi kasashen bakake ba, da suna da ilimi, amma a nan ne Saudiyya zata aiko kudi, ta koya wa malamai kin juna, su kuma yi wa'azin cewa jinin wane ya halasta, yan Izala samari kuwa su far ma 'yan shi'a su kashe su a unguwanni, dukkaninsu kuwa 'yan jiha daya ne zaka samu.
A yanzu, bayan da gwamnati ta kama malaminsu, 'yan shia masu son su kwato shi ta karfi, sun bazama Abuja neman shahada, abin takaici kuma, gwamnati ta biye musu tana kashe su din.
Duk da sauran 'yan Najeriya bamu jin dadin kisan gillar, wasunmu kuma basu fahimci me shia ke so ga Najeriya ba, kamar masu zurfi a Izala, irinsu Boko Haram da Alqaida, 'yan shia na son sai sun kore gwamnati ta dimokuradiyya, ta wai dagutu, sun kafa irin tasu mai malami da karfinsa ya fi shugaban kasa karfi, malamin kuwa zasu so ace jikan annabi ne, irin su Khomaini ko Khamenei, wadanda ke sanya bakin rawani sabanin fari.
Tun bayan da annabin Islama yace Ali ne zai mulki musulmi bayan ya mutu, aka sami bullar shia, watau shi'atu Ali, maimakon su Abubakar da Umar da Usman, da ma su Mu'awiyya Umayyawa da Abbasiyyawa, wadanda shi'a ke kira duk 'yan juyin mulki.
Zamunna sun shude, an yi kashe-kashe, kuma ana kai a Syria da Iraqi, da Yemen harma cikin Saudiyya, kan lallai sai wadannan Ahlul baiti sun karbi mulki daga hannun Sarakunan Saudiyya, wanda yasa abin har yake fallatsa kasashe irinsu Najeriya.
'Yan Shia dole su gane:
1. Babu ruwan Najeriya da wasu Ahlul baiti ko wasu da aka yi wa kwace a zamanin annabi.
2. Ali ya mutu, Husaini ya mutu, babu wata rigima da zata dawo dasu.
3. Khomaini ba dan Najeriya bane, haka ma Khamenei, komi alakarsu da Annabi, ba ruwanmu dasu.
4. Duk yadda muke tausayinsu baza mu iya hana gwamnati kashe su ba.
5. Zamu yi kokarin wayar dasu, kuma muyi kokarin gaya wa gwamnati a bi a hankali, domin masu neman shahada na iya zamowa 'yan Ta'adda muddin suka gaji suka dauki makami.
6. Ko an basu Sheikh Zazzaki ba zai iya kwatar Najeriya ba, komi tsawon zamani.
7. Iran baza ta taba turo sojojinta su taimaki 'yan shi'a, sai dai ta basu makamai da kudi, Iran Harami uku take so ta kwace daga Israila da Saudiyya.
8. Babu wata lahira da ake zuwa duk zuqi tamalle ce, in ka mutu garin kundumbala, kawai zaka koma yadda kake ne kafin a haife ka, babu kai sam.
9. Duk mai so ya kafa gwamnatin Allah yaje Saudiyya ko Iran ko Iraqi ko Yemen. Hanya a bude take.
10. Idan akwai damar a yi karatun Boko, yafi kyau a yi shi, ba sai an zama almajiran Malam ba ake cin nasara a rayuwa.
Gwamnati ya kamata ta san:
1. Ta daina biyewa 'yan Izala tana kashe samarin Shia mazansu da matansu.
2. Ita uwa ce ga kowa, Shia, Sunna, Darika, Kirista, Bamaguje, da Mulhidi.
3. A basu Malaminsu, amma a aika shi Iran exile yayi zaman gudun hijira na din-dindin.
4. A toshe duk wasu tashoshin Hausa dake yada akidar shia da Hausa, suna nan a satellite kyauta birjik daga Iran kai tsaye.
5. A tsawatar wa da Iran da Saudiyya kan tsoma baki da koyawa yaran Najeriya rikici da gwamnati, Iran ta haifar da Shia, Saudiyya ta haifar da Boko Haram.
6. Dole kasashen nan su biya kudin barna da akidunsu suka sanya mu a ciki, a je kotun duniya ta ICC a shigar da qara.
7. Dole a haramta almajirta, ko ta shia ko ta sufanci ko ta izala.
8. A daina kashe 'yan shia, in sunyi zafin kai ayi ta kama na gaba-gaba ana ajje su a wuraren da za'a wayar musu da kai.
9. A kyautata ilimin Boko da tsarin Sakulanci, wanda ya raba gwamnati da bin duk wani addini.
10. A halbe duk wanda ya dauki makami, kar ayi sulhu dashi.
Jama'ar Najeriya su sani:
1. Ba samarin shia ne matsala ba, akidar ce matsala, a rarrabe tsakaninsu.
2. A daina bin malami daya zalla, ko a wanne addini ne.
3. A daina murna in an ga an kashe dan shia, suma mutane ne, wayau kawai manyansu suka yi musu tun suna kanana, abin da ake kira indocrination a turance.
4. A baiwa ilimin Boko muhimmanci fiye da shaci fadin addinai.
5. A daina bata wa juna suna da sunan farantawa kasashen waje.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng