Dan gidan Gaddafi, Saiful Islam zai yi takarar shugaban kasa a Libya
- Saiful Islam ya tsira bai mutu ba a yakin da aka yi a kasar a 2011
- Yana neman shugabancin kasar
- Ana ganin zai iya hado kan kasar

Asali: Twitter
Tun bayan da aka kashe uba nai, Mu'ammar Ghaddafi, tsohon shugaban Libya, wanda ya shekara kusan 40 a kan mulki har 2011, wanda aka tayar masa da juyin-juya hali, kasar tasa ta Lbiya ta zama matattarar 'yan ta'adda daga kasashe da dama.
Yanzu dai, babban dan Ghaddafin wanda ya tsira ba'a kashe shi ba, yace yana da aniyar tsaya wa takarar shugabancin kasar, a bana, lamari da ake gani ka iya juyo akalar kasar daga yakin basasa da satar mai da ta'addanci.
DUBA WANNAN: Dole albashi ya kai N30,000 ko a ji a jika - NCL
A gwamnatance dai, kasar ta kasu kashi biyu ne, gabas da yamma, bangaren masu zafin kishin Islama kamar su ISIL da Al-Qaida, wadanda suka ci zabe a Tarabulus, da Khalia Haftar a Gabas, tsohon Janar din Ghaddafi, wanda ya kwaci Benghazi da sauran yankuna, kuma kasashen duniya suka karbe shi a matsayin halastacce.
In Saiful Islam Ghaddafi ya ci zabe, to kuwa ko tantama babu zai yi kokarin hado kan kasar, ya kuma dawo da ita yadda take a da, karkashin mahaifinsa, domin dama shi ke jagorancin ma'aikatun sirri da tsaro a kasar, yake kuma burin gadar Uban nasa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng