El-Rufai na kokarin kwatar kujerana ne don ya hau a karshen mulkinsa – Shehu Sani
Dan majalisa mai wakilitar al’ummar mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana makasudin da yasa gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ke kokarin ganin bayansa a siyasance, inda yace batu ne na kujerar da yake kai.
Majiyar LEGIT.com ta ruwaito Sanatan na cewa El-Rufai na yakarsa ne domin ya gaje kujerar Sanatan da yake kai, idan ya kammala wa’adin mulkinsa kamar yadda yawancin gwamnonon Najeriya suke yi, inda suka mayar da majalisar dattawa wajen ritaya.
KU KARANTA: Wani dan majalisan PDP ya tsallake rijiya da baya yayin da yan bindiga suka bude masa wuta
Shi dai Sanata ya fuskanci babbar kalubale ne a yayin zaben fidda gwani na takarar kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya, inda yake takara da wani na hannun daman El-Rufai, Uba Sani, kuma akwai yiwuwar Uba Sani zai kada Sheh Sani, sai dai uwar jam’iyya na goyon bayan Shehu Sani, ta ce shine kadai dan takararta.
Amma gwamnan El-Rufai da jam’iyyar APC reshen jahar Kaduna sun nuna rashin amincewarsu da wannan mataki da Uwar jam’yya ta dauka akan Shehu Sanin a hana kowa shiga takarar neman kujerarsa, har ta kai Uba Sani ya garzaya kotu akan haka.
Sai dai daga karshe uwar jam’iyyar ta sauko daga matakin daya dauka, inda ta baiwa Uba Sani tikitin tsayawa takarar Sanata bayan ya lashe zaben fidda gwani da aka yi, zaben da Shehu Sani ya kauracewa. Hakan ya sabbaba ficewarsa daga jam’iyyar ya koma jam’iyyar PRP.
Ficewarsa keda wuya sai aka jiyo Sanatan yana tsokaci game da ficewarsa daga APC, inda yace El-Rufai ya fi karfin shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomole, don haka ya kasa shawo kan matsalar dake tsakaninsa da El-Rufai, sai dai ya karyata neman a bashi takara kyauta.
“Ban taba neman a bani tikitin takara kyauta ba, a watan Yuli an samu yan majalisan da suka fice daga jam’iyyar, har da ni a ciki, amma Buhari da Tinubu suka hana ni fita, suka kuma bani tabbacin zasu shawo kan matsalar dake neman korata daga APC.” Inji shi.
Daga karshe ya bada tabbacin APC za ta fadi zaben 2019 idan ta cigaba akan wannan turna na rashin adalci, saboda a cewarsa jam’iyyar ta daukan ma yan Najeriya alkawurra da dama, amma bata cika musu ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng