'Yan bindiga sun sace tagwayen 'yan mata kwanaki kadan a daura musu aure

'Yan bindiga sun sace tagwayen 'yan mata kwanaki kadan a daura musu aure

- An sace wasu tagwayen 'yan mata a garin Duran da ke jihar Zamfara daf da daura musu aure

- Masu garkuwa da mutanen sun bukaci mahaifin 'yan matan ya biya N150 miliyan kudin fansa

- 'Yan matan sun ziyarci 'yar uwarsu ne a garin Duran inda masu garkuwa da mutanen suka afka gida su kayi awon gaba da su

A ranar Talata ne 'yan bindiga su kayi awon gaba da wasu tagwayen 'yan mata wanda ake daf da daura musu aure da kuma yayarsu a kauyen Duran da ke karamar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.

Hassana da Hussaina masu shekaru 16 wadanda za a daura wa aure ranar 16 ga watan Disamban wannan shekarar sun tafi kauyen Duran ne domin ziyarar yayarsu yayin da 'yan bindigan suka sace su.

'Yan bindiga sun sace tagwayen 'yan mata kwanaki kadan a daura musu aure
'Yan bindiga sun sace tagwayen 'yan mata kwanaki kadan a daura musu aure
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

An ce sun ziyarci yayarsu Summaya ne domin cigaba da shirye-shiryen daurin aurensu.

Alhaji Abubakar Yusuf, mahaifin 'yan matan uku ya bayyana cewa 'yan bindigan sun kutsa gidan Summaya ne suka kuma tafi da 'yan matan uku.

Ya ce 'yan bindigan da su kayi garkuwa da 'yan matan sun tuntube shi a waya inda suka bukaci ya biya kudin fansa N150 miliyan idan yana son ya sake ganin 'ya'yansa.

Mataimakin ciyaman din karamar hukumar, Alhaji Abubakar Duran ya ce yan bindiga sun sace fiye da mutane 15 a unguwani 5 da ke makwabtaka da kauyen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164