2019: Kotu ce kawai zata bayyana abinda zai faru da 'yan takarar APC na Zamfara - INEC
- INEC ta ce kotu ce kawai za ta iya tilastawa hukumar karbar sunayen 'yan takarar APC na jihar Zamfara
- Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu a yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi
- INEC ta ki haramtawa jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara gabatar da 'yan takara ne saboda sun rashin mika sunayen 'yan takarar kan lokaci

Asali: Depositphotos
A yau Juma'a na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa (INEC) ta sake nanatawa cewar ba ta karbi sunayen 'yan takarar zabe na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba daga jihar Zamfara.
INEC ta haramtawa jam'iyyar gabatar da 'yan takara a jihar ne sakamakon gazawarsu na mika sunayen 'yan takarar cikin wa'addin da hukumar ta bayar domin gudanar da zaben cikin gida da mika sunayen 'yan takara.
DUBA WANNAN: Duk mai son kwanciyar hankali, kar ya je kotu - Alkalin Alkalan Najeriya
Ciyaman din INEC, Farfesa Mahood Yakubu ya shaidawa manema labarai cewar a halin yanzu wuka da nama na hannun kotu a kan batun amincewa da karabar sunayen 'yan takarar na Zamfara ko akasin haka.
Yakubu ya kara da cewar hukumar ta fara wallafa sunaye da kadarorin da 'yan takarar da jam'iyyunsu suka mika sunayensu suka mallaka kamar yadda sashi na 31(30) na dokar zabe na 2010 ya tanada domin bawa al'umma daman sanin wadanda za su zaba.
Hukumar ta INEC ta kuma bayyana cewa jam'iyyun siyasa 79 ne suka mika sunayen 'yan takarar shugabancin kasarsu.
Shugaban ya ce baya ga sunayen 'yan takarar shugaban kasa 79 da aka gabatarwa wa hukumar, jam'iyyu 89 kuma sun gabatar da sunayen yan takara 1,803 domin takarar kujerar sanata da kuma sunyen 'yan takara 4,548 domin takarar mazabu 350 na tarayya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng